Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya bayyana kyakkywar fatan cewa Nijeriya da ‘yan Nijeriya za su farfado tare da girgijewa daga kalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta a halin yanzu sakamakon cire tallafin man fetur, yayin da gwamnati ke daukar kwararan matakai na samar da tallafi ga jama’a.
Yahaya ya bayyana haka ne a garin Kaltungo yayin da yake jawabi a wajen liyafa da nadin Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi a matsayin ‘Madakin Kaltungo’.
Ya kuma yi kira ga shugabanni da masu hannu da shuni a cikin al’umma da su tallafawa mabukata da masu karamin karfi.
Gwamna Inuwa ya kuma yi kira ga al’umma su kasance masu hakuri da goyon bayan manufofi da tsare-tsaren gwamnati don ci gaban al’umma.
“Babu wanda ya yi hasashen fadawa irin wannan mawuyacin hali, amma abun farin ciki shi ne yadda jama’a suke nuna juriya a irin halin da ake ciki, don haka muna rokon kara hakuri da fahimtar juna don ta yadda kowa zai ba da tashi gudummawa. Gwamnati ta shirya tsaf don samar da shugabanci nagari ga al’umma.”
Gwamnan ya yabawa Mai Martaba Mai Kaltungo Engr Saleh Muhammad bisa karrama Sakataren da babbar sarautar Madakin Kaltungo, da ɗokacin al’ummar masarautar bisa nuna jin daɗinsu na sake naɗa Njodi a matsayin Sakataren Gwamnatin jihar.