Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau cewa, yunkurin kasar Amurka na kakaba takunkumi kan wasu mutane da kamfanonin kasar, na da nufin dakile ci gaba da kwanciyar hankalin jihar Xinjiang da ma dakile ci gaban kasar Sin.
Ma’aikatar ta bayyana haka ne ta bakin kakakinta, inda ta ce zargin tilasta kwadago a jihar Xinjiang, karya ce tsagwaronta da masu kin jinin Sin suka shirya domin bata mata suna.
Wannan martani ne ga rahotannin dake cewa Amurka ta kara wasu kamfanonin Sin cikin jerin wadanda take zargi da tilasta kwadago.
Ma’aikatar ta ce Sin na yin tir tare da adawa da matakin na Amurka, kuma za ta dauki tsauraran matakan kare halaltattun hakkoki da muradun kamfanoninta. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp