Cristiano Ronaldo ya zura kwallo da kai a cikin mintuna na 87 don tura tawagarsa zuwa gasar cin kofin zakarun kungiyoyin Larabawa.
Al Nassr na bukatar kaucewa shan kashi domin samun cancantar zama ta biyu a rukunin C na gasar. Sai dai kuma.
- Takaddamar Da Ta Kunno Kai Lokacin Tantance Ministocin Tinubu
- Tinubu Ya Janye Sunan Maryam Shetty Cikin Ministoci
Bangaren Luis Castro ya yi dab da fitar da Al Nassr bayan Zizo ya ci wa Zamalek kwallo a minti na 53 da fara wasan.
Mintuna sun shude kuma ‘yan wasan Cristiano Ronaldo sun kasa samun bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Kafin Ronaldo wanda ya lashe Ballon d’Or sau biyar ya bayyana a lokacin da aka fi bukatarsa.
Ghislain Konan ya karbi kwallon a gefen hagu kuma ya tarar da dan wasan na Portugal ta hanyar giciye masa kwallon.
Yayinda Ronaldo ya doke Mohamed Sobhi ya kuma jefa kwallon da kai.
Bugu da kari, daya daga cikin muhimman ‘yan wasan kungiyar bayan tsohon dan wasan Real Madrid, Sadio Mane ya fara taka leda bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.