Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, ta ce ta kwace lasisin gudanar duk wasu ‘yan wasa da jarumai ciki har da daraktoci, gidajen gala da masu tallan maganun-uwan gargajiya da furodusoshi a masana’antarta ta shirya fina-finai ta Kannywood.
Shugaban hukumar, Abba Al-Mustapha ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne da nufin tsaftace masana’antar da kuma tabbatar da duk wanda ke ci-kin na samun cikakken takardu.
Al-Mustapha ya ce dole ne dukkan fitattun jarumai da furodusoshi su sabunta la-sisin yin aiki a masana’antar da hukumar tace fina-fanai ta Jihar Kano, domin kyau-tata sana’ar da kuma kauce wa gurbatattun da ke zubar da kimar sana’ar.
“Mun soke duk wasu lasisi na kungiyoyin masana’antar don samun takardun da kuma samun ingantattun tsare-tsare wadanda za su magance wasu matsalolin da ke cikin masana’antar.
“Muna da kungiyoyi kusan 13, mun kwace dukkan lasisinsu, wanda hakan ya ba mu damar tsaftace masana’antar, kafin a ba ko wani mutum lasisi dole ne mu gamsu da nagatarsa tare da sanin waye shi.
Al-Mustapha ya ce wannana mataki ta shafi dukkan mawaka da sauran masu nisadantarwa a masana’antar Kannywood, dole ne su sabunta lasisinsu ta haka ne za su iya tsaftace masna’antar.
Sai dai kuma wannan matsayi na Al-Mustapha ya jawo suka daga mutane da da-ma, musamman ‘yan adawa wadanda suke ganin ana so a yi amfani da siyasa ce kawai domin musguna wa wasu ‘yan fim da ba su goyi bayan gwamnati mai ci ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp