Shekaru fiye da ashirin da suka gabata na taba yin wani nazari da ya ja hankalin masu karatu a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, wanda daga baya aka sake buga shi a wasu jaridun Hausa. A lokacin na yi rubutu ne game da illolin rabuwar aure, wanda na duba bangarori daban-daban, kama daga rayuwar iyalin da aka rabu, musamman yaran da aka haifa tare da kuma al’umma baki daya.
Abin da a karshen nazari na nuna cewa, kuskuren da wasu ma’aurata ke yi shi ne suna duba matsalar kansu ce kawai ba sa tunani kan abin da zai iya biyo baya ba, a karan kansu ko kuma ga iyalin da za su bari cikin kunci. Babu shakka, ba duk ma’auratan da ke rabuwa ne, suke yanke hukunci ido rufe ba, wasu kan dauki lokaci ana nazari da auna abubuwan da za a iya samun maslaha a kansu, har sai abin ya kure ne sannan ake hakura a yanke shawarar rabuwa gaba daya.
- Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Neja Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa
- Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Fengyun-3
Wasu ma da ke rayuwar birane ko ‘yan boko, za ka ga har wajen kwararru ake zuwa, wato masana ilimin zamantakewa da sasanta tsakanin ma’aurata, don neman shawara da shiga tsakani, ana kashe makudan kudade, don dai a kaucewa rabuwa da juna a ceto aurensu da ke gab da rushewa. Don haka ba za mu zargi duk masu yanke shawarar rabuwa da juna a kan masu rashin hankali ko tunani ba. Za mu ba su uzuri kan cewa, mai yiwuwa abin da ya koro bera cikin wuta ne ya fi wutar zafi.
A makon da ya gabata na samu labarin rabuwar auren da ya girgiza ni matuka, har iyali biyu, wadanda a baya na san suna zaune lafiya da juna ko kuma dai ana zaune cikin kyautatawa da hakuri da juna. Kusan dukkansu sun kasance cikin aure kimanin shekaru goma sha takwas ko kusa da haka, sun haifi yaran da suka girma suka fara mallakar hankalin kansu. Amma kwatsam, sai muka ji ai sun rabu da juna. Daya daga cikinsu wanda babu laifi idan na ambaci sunansu a nan kasancewar labarin rabuwar ya yi yawo a jaridu da sauran kafafen sadarwa, shi ne rabuwar auren Malam Al-Ameen Ciroma, dan jarida kuma jarumin finafinan Hausa a Masana’antar Kannywood, da tsohuwar matarsa Wasila Isma’il, wacce ita ma tsohuwar jarumar finafinan Hausa ce.
An ma bayyana cewa; aurensu shi ne mafi dadewa a cikin auratayyar da aka yi tsakanin jaruman masana’antar. Koda yake, kawo yanzu ba ni da masaniya kan dalilan da suka haifar da rabuwa a dukkan auren da nake magana a kai, amma har ga Allah na san su kansu da suka rabu suna cikin wani yanayi na alhini, da jujjuya abubuwan da suka faru a baya, ko suka janyo rabuwar aurensu, wanda za a iya cewa ya faru kamar a mafarki, kuma bisa kaddara. Ko kuma kamar yadda wasu ke cewa, yadda kowacce halitta ke da rai haka aure ma yana da nasa wa’adin, wanda idan ya zo karshe babu makawa sai an rabu. Za ta iya yiwuwa wani auren ya dade da rabuwa a zukatan ma’auratan, domin wasu abubuwa na auratayya a tsakaninsu tuni suka yanke, sai dai kawai ba a yanke hukunci da sanar da shaidu ba ne, sai da karshen wa’adin ya zo.
Wani auren kuma cike yake da zarge – zarge marasa dadi, da aibata juna ko jifan juna da sunaye iri-iri na batanci da muzantawa, alhalin a baya an nuna wa juna soyayya da kulawa. Wasu kuma dalilai ne na cin zarafi, zalunci, da tozartawa, inda za ka ji ana cewa ai da wannan zaman gara rabuwar saboda kada wani ya kashe wani, sakamakon azabtarwar da wani ke yi wa wani. Ko dai a rika nuna shi mijin ne yake dukan matarsa, da wulakanta ta, ko tauye mata hakkokinta da ke jefa rayuwarta cikin mummunan hali. Ko kuma ita matar ce take wulakanta mijin, aibata shi da cin zarafinsa, a wasu lokuta, walau da duka ko da harshenta. Tun mijin na boyewa har dai ya iya fitar da abin da ake yi masa a boye, jama’a su fahimci ukubar da yake ciki, amma ya kasa bayyanawa saboda ana ganinsa namiji, kar a gane gazawarsa.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa