Tawagar wakilan shugabannin kungiyar ECOWAS da na Majalisar Dinkin Duniya, a yau Talata sun garzaya zuwa Jamhuriyar Nijar domin tattaunawa da jagororin sojin kasar da suka kifar da gwamnatin mulkin dimokuradiyya a kasar. Â
Kafar dillancin labarai na kasar Faransa RFI ya ruwaito cewa, tawagar ta isa Niamey, babban birinin Nijar don tattaunawa da jarororin sojin da suka yi juyin mulkin a madadin sauran kasashen duniya.
- Saudiyya Ta Jagoranci Zaman Sulhu Tsakanin Rasha Da Ukraine
- Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Mace Ta Farko A Matsayin Babbar Alkalin Alkalai Ta Jiha
A cewar rahoton RFI, wannan yunkurin dai, na cikin kokarin da ake yi na sake dawo da kasar a kan turba biyo bayan yin juyin mulkin.
Kafar ta ruwaito wani jami’in Nijeriya ya ce, gwamnatin Nijeriya ta yi barazanar cewa, za ta bayar da rabin dakarun soji 25,000 domin a tura su zuwa Nijar, idan har bukatar hakan ta ta so.
Bugu da kari, kafar ta ce, su ma mahukuntan sojin kasashen Senegal, Benin da kuma Cote d’Ivoire, su ma za su tura nasu dakarun sojin zuwa Nijar domin yin aikin.
A ranar 26 na watan Julin 2023 ne, jagororin sojin da ke kula da fadar shugaban kasar ta Nijar suka yi juyin mulki a kasar, inda kuma suka tsare hamabararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, wanda kuma Janar Abdourahamane Tchiani da ya jagoranci juyin mulkin, ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa na mulkin soji.
Kazalika, sojin sun kuma rufe iyakokin kasar tare da dakatar da duk wasu ayyuka a hukumomin gwamnatin kasar suka kuma kakaba dokar hana fita.
Wannan juyin mulkin shi ne na biyar tun bayan da Faransa ta bai wa Nijar ‘yancin kai a 1960.
A ranar 6 ga watan Agusta, an kirga soji guda 57,000 da kuma guda 245,000 daga bangaren ECOWAS, inda kuma Faransa ta ki bayar da nata daukin.