Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, akwai tabbacin za ta kammala babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya nan da zuwa karshen 2022.
Shugaban kula da samar da manyan hanyoyi a Ma’aikatar Ayyuka Da Gidaje, Mista Mr Folorunsho Esan, ya sanar da haka a yayin da wasu jami’an ma’aikatar suka kai ziyarar kwana biyu don ganin yadda aikin ke tafiya a ranar Alhamis a Kaduna.
- Zelensky Ya Ja Hankalin Duniya Da Abubuwa Hudu Kan Yakin Ukraine
- Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi Yayin Bikin Cika Shekaru 25 Da Dawowar HK Kasar Sin Da Na Kaddamar Da Sabuwar Gwamnatin Yankin
Ya ce, ganin yadda akin ke tafiya lallai dan kwangilar zai kammala aikin a cikin wannan shekarar.
Ya kuma ce, dukkan mastalolin da ake tunanin fuskanta a yayin aikin an yi maganinsu.
A nasa jawabin Mista Theo Scheepers, wakilin kamfanin Julius Berger Nigeria Plc, ya ce tabbas za a kammala aikin hanyar a cikin wata shida masu zuwa, kasa da yadda aka kiyasta tun da farko.
Ya ce, Ma’aikatar Ayyuka ta taimaka musu kawar da dukkan matsalolin da suka fuskanta a yayin gudanar da aikin hanyar.
“Mun nemi hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki kamar su jami’an kananan hukumomi da shugabanin al’umma kuma sun bamu dukkan goyon baya, ta haka muka samu nasarar da ake bukata.” In ji Scheepers.