Matsaloli daban-daban ne ke haddasa rabuwar aure, kuma kowa da dalilinsa. Kamar yadda ake cewa, babu wani aure da ya yi kama da na wani to, haka ko a wajen rabuwa, za ka tarar kowa da nasa dalilin. Wani dalilin ma idan mutum ya ji sai ya yi dariya kafin ya fara tambayar garin yaya haka ta faru, domin dalili ne da za a iya sasantawa cikin ruwan sanyi a warware shi.
Wani kuma abubuwa da dama ne aka rika tara su har suka yi yawan da ba a iya warware su lokaci guda ba, sai dai a rabu idan ya so in suna da rabon sake komawa zaman aure a sake dawowa.
- Dan Siyasar Japan Yana Son Sake Jefa Al’ummar Taiwan Cikin Mawuyacin Hali
- Yadda Na Gano Angona Ya Yi Zina Da Wata A Ranar Daurin Aurenmu –Wata Amarya
A wajen wadanda suke da wayewar zamani su kan je har wajen alkali a raba zaman na wani lokaci, ba da nufin saki ba, sai dai don a bai wa kowanne bangare damar zuwa ya yi nazari da tunani, kuma a bai wa zuciya da tunani zarafin da za ta huce a samu natsuwa, kafin a koma a sake fuskantar juna. To, ko ma dai wanne dalili ne, ko wanne salo ne aka bi wajen rabuwar, za mu iya fahimtar cewa ba abu ne mai dadi rabuwar aure ba.
Saboda da zarar an yi aure an hayayyafa na tsawon wasu shekaru, ana dauka kan cewa an zama daya, ko da an rabu ba rayuwa ba za ta sake armashi kamar a baya ba. Nauye nauyen kula da yara da damuwa a kan karatunsu ko tarbiyyarsu, nan ma wata jarabawar ce.
Su kansu yaran da aka rabawa hankali, ko aka canza musu gida da makaranta, da abokan rayuwa suna shiga cikin damuwoyi iri-iri. Daga ciki akwai; matsalar tabarbarewar tarbiyya, shaye-shaye, rashin kokari a makaranta da gudun shiga mutane. Wani lokaci har da yawan zafin rai da shiga rigima, ko cin zalin wasu yaran. Abin takaici ne yadda wasu musamman mata ke bayyana cewa, su ne suka nemi a raba auren don sun gaji da ganin bakin ciki, sun gwammaci zaman zawarci da ci gaba da ganin wulakancin da suke cewa suna gani a gidajen aurensu. Alhalin kuwa addinin Musulunci ya tsawatar sosai kan matan da suke neman mazajensu na aure su sake su. Wani lokaci kuma wasu ne a cikin mata ake samu da suke hurewa ‘yan uwansu mata, masu hakurin zaman aure kunne, kan cewa su bar gidan, in ba so suke rayuwarsu ta lalace ba. Su rika karanto musu wasu abubuwa na rashin tabbas da kwadaitar musu da rayuwar ‘yanci da walwala a rayuwar zawarci. Sai bayan sun fito daga gidan miji su tarar da rayuwar ba a yadda suka zata ba. Kalilan ne a matan da suke barin aurensu don ganin suna shan wahala, suke sake samun wata damar ta sake yin aure ko kuma kafa wani kasuwanci da zai rika kawo musu riba, suna kula da kansu, da ‘ya’yansu.
Wasu kuwa sai dai gyaran Allah, rayuwar kara lalacewa take yi, har ma su gwammaci gara da a ce su koma dakin aurensu da zaman da suke yi na rashin tabbas, da yaudarar manema da ke jefa su a rayuwar zinace-zinace da sayar da mutunci. Ban sani ba ko saboda karuwar talauci da kuncin rayuwa ne, ya sa darajar aure ke kara zubewa a idanun wasu matan da ke ganin babu abin da aure ke tsinanawa rayuwar su in ba takaici da wahala ba, don haka ma za ka yi ta ji a maganganunsu da rubuce-rubucensu a yanar gizo, suna nuna gazawar aure da lalacewar maza, ko muguntarsu a cewar wasu matan, wanda ke sa suna jin auren yana fita a ransu. Kuma hakan ba ya rasa nasaba da yadda wasu mazan suke yi wa auren rikon sakainar kashi da sakewa mata da ‘ya’ya wahalhalun aure da kula da kansu. Nauyin da sharuddan kula da hakkoin aure suka dorasu kan maza.
Amma yanzu a mafi yawan gidaje mata ne ake bari da dawainiya mazan sun juya musu baya, babu ko tallafawa. Sai ka ga mace bazar-bazar kamar za ta yi hauka, tana fafutukar yadda za ta nemawa iyali abin da za su ci ko kudin makaranta, saboda uban wanda ya kamata ya zama jagora a gidansa halin yau da mutuwar zuciya sun sa ya yi watsi da bukatunsu. Lallai wannan rubutu, yana so ya kara zaburar da iyaye, musamman ma’aurata da su dubi girman Allah, su tsaya su kula da gyaran gidajensu, a daina watsi da hakkokin da Allah ya dora mana. A rika tausayawa juna ana kyautatawa, don a samu rabon duniya da lahira. Mata su daina sauraron wadanda suka fitar da tsammani daga samun jin dadin aure, hurewa wasu kunne don su ma su bi sahunsu suna gantali a titi, wanda babu inda zai kai su sai halaka.