Shugaban sojojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya bayyana dalilin da ya sanya su hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum inda ya ce, sun yi ne domin ceto jamhuriyar Nijar da Nijeriya daga wata barazana.
Duk da cewa, bai bayyana irin nau’in barazanar ba wacce ya yi ikirari, amma ya nemi afuwar mummunar tarbar da aka yi wa tawagar tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar wanda ya wakilci kungiyar ECOWAS zuwa Babban birnin Yamai kan tattaunawa a makon da ya gabata.
Shugaba Tchiani, ya bayyana hakan ne yayin da tawagar malaman addinin musulunci ta Nijeriya karkashin jagorancin Sheik Bala Lau, suka isa Birnin Yamai a karshen mako don nemu mafita ba ta hanyar amfani da karfin soji ba wajen dawo da mulkin Dimokuradiyya a Jamhuriyar Nijar.
Sun gana da Janar Tchiani na sa’o’i inda suka tattauna kan muhimman batutuwa ciki har da bukatar ECOWAS.
Malaman addinin Musulunci a makon da ya gabata sun gana da shugaban Nijeriya kuma shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, kan bukatar tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki don warware rikicin siyasar da ke tsakanin bangarorin biyu.
A bisa bukatarsu, Tinubu ya amince da Malaman da su gana da shugabannin sojojin Nijar domin sasanta rikicin cikin lumana.