Wasu ‘yan bindiga sun kashe ango da amaryarsa, wadanda dukkaninsu malaman makarantar sakandaren BECO Comprehensive High School ne da ke Kwi a karamar hukumar Riyom a jihar Filato.
‘Yan bindigar sun kuma raunata mataimakin shugaban makarantar.
- ‘Yan Majalisar Ghana Sun Gargadi Shugaban Kasar Kan Tura Sojoji Nijar
- ECOWAS Ta Gargadi Sojin Nijar A Kan Hukunta Bazoum
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
Alabo, wanda bai yi karin bayani kan lamarin ba, ya ce rundunar na bincike a kan lamarin.
Sakataren yada labarai na kungiyar Berom Youth Movement, Mista Rwang Tengwong, a wata sanarwa da ya fitar ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Litinin.
“Mun ji takaicin yadda ‘yan bindiga suka mamaye makarantar BECO Comprehensive High School Kwi.
“An harbe malamai biyu, Mista da Misis Rwang Danladi, wadanda ba su jima da aure ba.
“Mista Dalyop Emmanuel, mataimakin shugaban makarantar, ‘yan bindigar sun yi masa munanan raunuka.
“Malaman sun gudanar da taron tattara sakamakon daliban da bayar da lambobin yabo na makarantar na 2023 da aka shirya yi a wannan Juma’a.
“Wanda ya ji rauni a halin yanzu yana karbar magani a asibitin koyarwa na Jami’ar Jos,” in ji shi.
Kakakin ya yi tir da karuwar masu aikata laifuka a wasu yankuna na jihar.
“Muna kira ga jami’an tsaro da su hanzarta kai farmaki kan wadannan bata gari da suka zama gungun ‘yan ta’adda, musamman a Fass da Mahanga da ke Riyom.
“Wannan ya zama dole don kawar da masu aikata laifuka da suka saba wa doka da oda,” in ji shi.