A Talatar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, da su ci gaba da ingiza wayewar kai game da muhallin halittu, a matsayin sa na muhimmin aiki da aka sanya gaba.
Yau Talata 15 ga watan Agusta ce ranar bikin muhallin halittu, karon farko a kasar Sin, a kuma wannan gaba ne shugaba Xi ya ba da umarnin. Shugaban na Sin ya jaddada aniyar cimma manyan burikan nan 2, game da iskar Carbon mai dumama yanayi, wato kaiwa kololuwar fitar da Carbon din zuwa shekarar 2030, da kuma kawar da illar sa zuwa shekarar 2060.
Kaza lika shugaban ya yi kira ga al’ummar kasar Sin, da su ci gaba da sauya akalar rayuwa zuwa amfani da dabarun kaucewa gurbata muhalli, da rage fitar da iskar ta Carbon, a al’amuran su na yau da kullum.
Daga nan sai ya bayyana fatan sa na ganin daukacin al’ummar Sinawa ta maida hankali ga yayatawa, da zama abun misali a fannin rungumar manufar kasancewar ruwa mai tsafta, da tsaunuka masu dausayi, muhimman kadarori masu kima. (Saminu Alhassan)