• English
  • Business News
Saturday, June 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar CMG Da Kafafen Yada Labarai Na Afrika Zai Fahimtar Da Al’umma Kyakkyawar Aniyar Kasar Sin

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Hadin Gwiwar CMG Da Kafafen Yada Labarai Na Afrika Zai Fahimtar Da Al’umma Kyakkyawar Aniyar Kasar Sin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, da kungiyar kawancen gidajen rediyo ta Afrika, sun gudanar da taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwarsu, jiya Litinin a Nairobin kasar Kenya.

Muhimmancin kafofin watsa labarai a tsakanin al’umma abu ne mara misaltuwa, kasancewarsu tamkar gada tsakanin al’umma da wajen yankunansu. Kafar watsa labarai tamkar makaranta ce dake kan ilmantar da al’umma.

  • CMG Ya Sanya Hannu Kan Takardun Hadin Gwiwa Da Hukumar Sadarwar Wayar Tarho Ta Honduras

Hadin gwiwar CMG da kafafen yada labarai a nahiyar Afrika, musamman a irin wannan lokaci da karairaiyi da zarge-zarge suka kara yawa, zai taka gagarumar rawa wajen ilmantar da al’ummun nahiyar Afrika game da yanayin kasar Sin da kyakkaywar aniyarta gare su, har ma da dimbin tallafi da goyon baya da take ba nahiyar, haka kuma zai kara fahimtar da Sinawa ainihin yanayin da nahiyar Afrika ke ciki.

Rashin fahimta tamkar wata cuta ce dake bukatar kulawar likita. Yadda kafafen yada labarai na yammacin duniya suka yi kaka-gida a kasashenmu na Afrika, ya sa suke yada jita-jita da zummar haddasa fitina da shafawa Sin bakin fenti, domin cimma muradun kasashensu na babakere da dakile karbuwar kasar Sin a nahiyar.

Kyautatuwar alaka ko aminci mai karfi tsakanin Sin da kasashen Afrika, ya sa kafafen yada labarai na yammacin duniya ke kara wasa wukarsu na shafawa kasar Sin bakin fenti. Wannan ya sa nake ganin alaka ko kawance tsakanin kafafen yada labarai na Sin da Afrika ke da muhimmanci gaya, domin bangarorin biyu za su bayar da hakikanin labarai bisa yanayi na gaskiya da adalci ta yadda al’umma za su iya gane ainihin yanayin da duniya take ciki da ma wadanda ba sa son ganin ci gabansu.

Labarai Masu Nasaba

Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su

Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva

kamar yadda hadin gwiwar Sin da Afrika ke haifar da kyawawan sakamako a sauran fannoni, haka hadin gwiwa tsakanin CMG da kafafen yada labarai na Afrika zai yi kyakkyawan tasiri wajen fahimtar da al’umma game da irin kyakkaywar alakar dake tsakanin Sin da Afrika, domin su fahimci cewa, kasar Sin aminiya ce ta kwarai. Kana zai kai ga samun goyon bayan juna mai dorewa tsakanin al’ummomin, har ma da gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya. Bugu da kuma kari, zai dakile yunkurin masu kokarin lalata wannan kyakkyawar dangataka.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Tsadar Rayuwa: Tinubu Na Duba Yiwuwar Dawo Da Tallafin Mai Na Wucin Gadi

Next Post

Kungiyar Dattawan Arewa Ta Bukaci Tinubu Ya Gaggauta Janye Takunkumin Da Aka Kakabawa Nijar

Related

Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su
Daga Birnin Sin

Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su

16 hours ago
Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva

17 hours ago
Xinjiang Ta Bude Hanyar Jigilar Kayayyaki Ta Kasa Da Kasa Zuwa Afirka Ta Farko
Daga Birnin Sin

Xinjiang Ta Bude Hanyar Jigilar Kayayyaki Ta Kasa Da Kasa Zuwa Afirka Ta Farko

18 hours ago
Lai Cing-te Ba Zai Cimma Nasarar Kalubalantar Dokar Kasa Da Kasa Ba
Daga Birnin Sin

Lai Cing-te Ba Zai Cimma Nasarar Kalubalantar Dokar Kasa Da Kasa Ba

19 hours ago
Abin Da Ya Sa Muke Ci Gaba Da Tuntubar Kasar Sin A Kai A Kai
Daga Birnin Sin

Abin Da Ya Sa Muke Ci Gaba Da Tuntubar Kasar Sin A Kai A Kai

20 hours ago
An Watsa Shirin “Yawon Bude Ido A Tuscany” Da Cmg Ya Gabatar A Italiya
Daga Birnin Sin

An Watsa Shirin “Yawon Bude Ido A Tuscany” Da Cmg Ya Gabatar A Italiya

21 hours ago
Next Post
Kungiyar Dattawan Arewa Ta Bukaci Tinubu Ya Gaggauta Janye Takunkumin Da Aka Kakabawa Nijar

Kungiyar Dattawan Arewa Ta Bukaci Tinubu Ya Gaggauta Janye Takunkumin Da Aka Kakabawa Nijar

LABARAI MASU NASABA

Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu

Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu

June 28, 2025
Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Demokuradiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

Ƙoƙarin Ƙungiyoyin Afrika A Gasar Kofin Duniya

June 28, 2025
Bam Ya Kashe Mutane 4, Ya Jikkata 21 A Yobe

Bam Ya Kashe Mutane 4, Ya Jikkata 21 A Yobe

June 28, 2025
Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Demokuradiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Demokuradiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

June 28, 2025
Za a Binne Ɗantata A Madina, Za Ai Yi Sallar Ga’ibi A Kano

Za a Binne Ɗantata A Madina, Za Ai Yi Sallar Ga’ibi A Kano

June 28, 2025
Me Ya Sa Syria Ta Bari Ana Amfani Da Sararin Samaniyarta Wajen Kai Wa Iran Hari?

Me Ya Sa Syria Ta Bari Ana Amfani Da Sararin Samaniyarta Wajen Kai Wa Iran Hari?

June 28, 2025
Wace Nahiya Ce Ta Fi Iya Ƙwallon Ƙafa Tsakanin Turai Da Kudancin Amurka?

Wace Nahiya Ce Ta Fi Iya Ƙwallon Ƙafa Tsakanin Turai Da Kudancin Amurka?

June 28, 2025
Ƙasashen Afrika 10 Da Suka Fi Girman Kasafin Kudi A 2025

Ƙasashen Afrika 10 Da Suka Fi Girman Kasafin Kudi A 2025

June 28, 2025
Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi Reshen Kaduna Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Matafiya A Filato

Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi Reshen Kaduna Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Matafiya A Filato

June 28, 2025
Shahararren Ɗan Kasuwa Aminu Dantata Ya Rasu

Shahararren Ɗan Kasuwa Aminu Dantata Ya Rasu

June 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.