Albarkacin ziyarar da shugabar kasar Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento ke yi a kasar Sin, daraktan babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG Shen Haixiong, tare da ministan harkokin wajen kasar Honduras Eduardo Enrique Reina, sun sanya hannu kan takardun hadin gwiwa, tsakanin CMG da hukumar sadarwar wayar tarho ta Honduras, a yau Litinin 12 ga wata a birnin Beijing.
Shugaba Xi Jinping na Sin, da takwarar sa ta Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento, sun halarci bikin sanya hannu kan takardun hadin gwiwar. (Saminu Alhassan)
Talla