Yanzu haka babban batu dake damun al’ummar duniya shi ne, batun abinci, matsalar dake ciwo wasu sassan duniya tuwo a kwarya sakamakon fadace-fadace, matsalar fari, ambaliyar ruwa da ta yi awon gaba da amfanin gona ko wasu matsaloli masu nasaba da matsalar sauyin yanayi ko wasu bala’u daga indallahi. Wannan ya sa ake kira ga kasashen duniya su ba da muhimmanci ga batun samar da abinci, da kuma neman ingantacciyar hanyar warware matsalar ta hanyar hadin gwiwar kasa da kasa.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya fada a kwanakin baya cewa, tsarin samar da abinci na duniya “ya tabarbare”, kuma dole ne a canza hanyar samar da abinci, da kuma yadda ake amfani da shi.
A shawarar da ya gabatar game da raya kasa da kasa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanya batun samar da abinci a matsayin daya daga cikin muhimman fannoni takwas na hadin gwiwa. Kuma kasar Sin ta gudanar da hadin gwiwa a fannin aikin gona tare da kasashe da yankuna fiye da 140, da inganta fasahohin aikin gona sama da 1,000 ga kasashe masu tasowa, lamarin da ya haifar da karuwar yawan amfanin gona da kashi 30 zuwa 60 cikin 100 a yankunan da ake aikin.
Baya ga wannan kuma, kasar Sin ta horar da kwararru fiye da 14,000, masu sana’ar noman shinkafa mai aure ga kasashe masu tasowa sama da 80, ta kuma gina kauyukan gwaji na bunkasa aikin gona, da rage talauci masu tarin yawa, wanda hakan ya taimakawa kasashe masu tasowa, wajen kara kwarewar inganta ayyukan noma da samar da abinci.
Bayanai na nuna cewa, duk da wadannan matakai akwai tarin jama’a a sassan duniya dake fama da yunwa sakamakon wasu matsaloli ko dalilai ko matakan kashin kai da wasu kasashen yamma suka dauka. Matakai da tsare-tsare da kasar Sin ke bijiro da su karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, sun taimaka matuka wajen kara samar da abinci da ma dabarun noma iri-iri a sassan nahiyar.
Masana na cewa, kasashen Afrika za su iya yin amfani da huldar dake tsakanin Sin da nahiyar, wajen kawo gagarumin sauyi a tsarin aikin gona, da magance yunwa, da karancin sinadarai masu gina jiki, da kuma habaka tattalin arzikin mazauna yankunan karkara.
A cewar shugaba Xi jinping na kasar Sin, dalilin da ya sa JKS mai mulkin kasar ke samun cikakken goyon baya daga al’ummar kasar shi ne, tana tsayawa kan kokarin tabbatar da ingancin rayuwar jama’a, musamman manoma.
Wannan na nuna cewa, idan har ana son wadatar da kasa da abinci, ya kamata mahukunta su taimakawa manoma don su samu karin kudin shiga, da raya kauyuka, da kuma ci gaba da zamanintar da aikin gona. Sanin kowa ne cewa, abinci shi ne tushen rayuwa. Kamar yadda malam Bahaushe ke cewa, sai da ruwan ciki ake jan na rijiya. kuma sai ciki ya koshi kafin a iya yin komai na rayuwa.