Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta amince da bayar da Naira Biliyan 5 ga kowace Jiha a matsayin tallafi don rage radadin cire tallafin man fetur.
An dauki wannan matakin ne a zaman majalisar da aka yi a ranar Alhamis a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima wanda gwamnonin jihohi da sauran mambobin majalisar suka halarta a fadar gwamnati da ke Abuja.
Idan za a iya tunawa, a ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban kasa Bola Tinubu a jawabinsa na rantsar da shi ya sanar da kawo karshen bayar da tallafin man fetur.
Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Abdulrahman Abdulrazak (Kwara), Hope Uzodinma (Imo), Inuwa Yahya (Gombe) Dauda Lawal (Zamfara), Dr. Alex Otti (Abia), Babajide Sanwo-Olu (Lagos) da Ademola Adeleke (Lagos).
Sauran sun hada da Sanata Bala Mohammed (Bauchi), Sanata Uba Sani (Kaduna), Sheriff Obrevwori (Delta), Charles Soludo (Anambra), Godwin Obaseki (Edo), Yahaya Bello (Kogi), Umaru Namadi (Jigawa),
Haka kuma a taron akwai Gwamna Umo Eno (Akwa Ibom), Prince Bassey Otu (Cross River), Lucky Aiyedatiwa (Mukaddashin Gwamnan Jihar Ondo), Dapo Abiodun (Ogun), Ahmad Aliu (Sokoto), Agbu Kefas (Taraba), Abdullahi Sule. (Nasarawa), Peter Mbah (Enugu), Babagana Zulum (Borno)
Mataimakan gwamnonin jihohin Katsina, Ribas, Yobe, Adamawa, Kano, da Kebbi duk suma sun halarci taron.