‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi 22, sun bukaci Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Rt. Hon. Abubakar Y Sulaiman da cikin ruwan sanyi ya amince ya yi murabus ba tare da bata wani lokaci ba ko su tsige shi nan ba da jimawa.
‘Yan majalisar a karkashin jagorancin mataimakin shugaban masu rinjaye, Baballe Abubakar Dambam mai wakiltar mazabar Dambam/Dagauda/Jalam, a ranar Juma’a sun jefa kuri’ar rashin kwarin guiwa kan jagororin majalisar bisa abun da suka kira rashin iya tafiyar da harkoki jagoranci yadda ya dace.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida bayan kammala zaman nasu, Baballe ya ce “Za mu dauka daga yau Juma’a’ babu jagoranci a majisar dokokin Jihar, ina daga cikin jagororin amma mun ji a ranmu cewa yanzu ne ya dace mu yi hakan. Don haka mun kada kuri’ar rashin gamsuwa da dukkanin jagororin majalisar dokokin Jihar Bauchi.
“Muna kira ga shugabannin majalisar da su yi murabus cikin ruwan sanyi su mika takardun ajiye aiki ga akawun majalisa kawai, don samun damar gudanar da sabon zaben shugabanni.”
Mambobin sun bukaci gwamnatin jihar Bauchi a karkashin jagorancin Bala Muhammad da kada su dauka zagon kasa suke shirya wa gwamnatin jihar, illa kokarin da suke yi na ganin an samu gyara cikin lamuran da suka shafi majalisar.
“Muna son a samu gyara ne domin muddin aka ci gaba da tafiya karkashin jagorancin da ke a nan yanzu babu wani abin da ke tafiya yadda ya dace. Muna tabbatar wa gwamna cewa canjin da za a samu a majalisar ba zai shafi akalar majalisar dokokin Jihar da bangaren gwamnatin ba.”
Kazalika, mambobin majalisar sun nuna damuwarsu bisa yadda aka samu koma baya wajen tafiyar da harkokin aikin hajji na gaza gudanar da tsare-tsaren da suka dace a hajjin bana.
Sun kuma nuna damuwarsu yadda ba a kula da su ba wajen rabon kujerun zuwa Makkah duk kuwa da cewa kakakin majalisar jihar shi ne mataimakin shugaban kwamitin tsare-tsaren na aikin hajjin.
Da yake maida martani kan wannan matakin, babban mai bai wa gwamna shawara kan harkokin majalisa, Sani Mohammed Burra, ya ce matsalolin da aka samu kan aikin hajji a bana ba jihar Bauchi ce kadai abun ya shafa ba, ya ce kasa ne baki daya sakamakon karancin adadin kujeru da aka ware wa jihar.
Dangane da rikicin da ya kunno kai a majalisar kuwa, ya ce rikicin cikin gida ne kuma za a shawo kansa nan kusa.