Makiyaya a garin Jos da ke Jihar Filato, na ci gaba da nuna damuwarsu biyo bayan gano bullar cutar da ke harbin dabbobi (Anthrax) daga Jihar Neja.
“Akwai bukatar daukan matakan gaggawa yadda ya kamata domin dakile yaduwar cutar zuwa wannan gari namu na Jos.”
Haka zalika, Ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta tarayya ce ta sanar da bullar wannan cuta da aka gano a Jihar ta Neja a makon da ya gabata, inda gano bullar cutar ya sanya makiyayan na garin Jos shiga matukar tashin hankali.
Harwa yau, a ranar 14 ga watan Yulin 2023 ne Ofishin babban likitan dabbobi na kasa ya tabbatar da gano alamomin wannan cuta (Anthrax), a wata gona da ke Karamar Hukumar Suleja Jihar Nejan.
Wannan gona da ke garin Gajiri, daura da babban titin Abuja zuwa Kaduna a Karamar Hukumar Suleja, na dauke da rukunin dabbobi iri daban-daban da suka hada da Shanu, Akuyoyi da sauran makamantan su.
Biyo bayan bullar cutar a wannan gona ne, ya sanya wasu daga cikin makiyaya da sauran masu kiwo a garin na Jos shiga dimuwa da furgici tare da yin kiraye-kiraye don ganin an dakile ci gaba da yaduwarta.
“Ina da masaniya kwarai da gaske a kan wannan cuta, sannan ko shakka babu ina cikin matukar damuwa tun daga lokacin da na samu labarin tabbacin bullar ta a Jihar Neja,” a cewar wani makiyayi a Jos, Muhammad Rabi’u.
Muhammad ya ci gaba da cewa,“ ina kiwon shanu da tumaki, sannan a garken nasu nake kwana. Don haka, wajibi ne na kasance cikin firgici da damuwa.”
Daga nan ne, sai ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Filo da ta gaggauta daukar matakan da suka dace domin dakile yaduwar a fadin jihar baki-daya.
Shi ma wani makiyayin mai suna Babangida Musa ya bayyana nasa ra’ayin cewa, tun fil azal akwai wannan cutar, ba wai yanzu ba ne ta fara bayyana, sai dai kawai a kara tsaurara bincike tare da kokarin ganin an magance ta, ba ma a garin na Jos kadai ba, har ma fadin kasa baki-daya.
“Muna iya bakin kokarinmu na ganin wannan cuta ba ta ci gaba da yaduwa a wannan gari namu na Jos ba, sannan muna kuma yin kira ga Gwamnatin Jihar Filato, don sake ci gaba da dage damtse wajen daukar matan gaggawar day a kamata domin dakile yaduwar ta,” in ji Babangida.
Kazalika, wani makiyayin daga Jihar Neja mai suna Malam Muhammad ya karkare da cewa, “Bayan samun labarin bullar alamomin wannan cuta a Jihamu ta Neja, mun yi matukar kaduwar tare da shiga razani. Don haka, muke kira ga gwamnati da babbar murya don dakile ci gaba da yaduwar cutar a sauran gurare daban-daban.”
“Muna rokon Gwamnatin Jihar ta Filato da ta dakile yaduwar cutar zuwa cikin jihar, musamman ma cikin garin Jos da kewayensa. Muna kuma addu’ar kada cutar ta ci gaba da yaduwa sauran jihohin da ke a fadin wannan kasa,” in ji shi.