An zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (NNPP) a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, da yin aikin da bai dace ba a jam’iyyar ta NNPP a zaben da ya gabata na 2023.
Politics Digest ta rawaito cewa, hadakar shugabannin jam’iyyar na jihohi ne suka yi wannan zargin.
- Ganduje Ba Zai Hana Kwankwaso Shiga APC Ba
- Shugabanni Sun Bukaci Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP Kan Zargin Yi wa Jam’iyyarsu Zagon Kasa
Shugabannin jam’iyyar NNPP na jihar sun yi ikirarin cewa Kwakwaso na yin yunkurin yin lalata tsarin jam’iyyar, inda suka yi zargin cewa yana amfani da ‘ya’yan jam’iyyar wajen aikata laifuka da kuma daukar matakin da bai dace ba.
Sun kuma zargi babban kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa da rusa majalisun zartarwa na jam’iyyar ba bisa ka’ida ba a jihohi 10 na Nijeriya.
Da yake jawabi ga manema labarai a Ado-Ekiti, a jiya, mai magana da yawun kungiyar shugabannin, Dada Olayinka Olabode, wanda kuma shi ne shugaban NNPP na jihar Ekiti, ya ce an dauki matakin shari’a kan Kwankwaso da kwamitin gudanarwar jam’iyyar.
Ya ce: “Mun dauki matakin shari’a don magance wannan rashin adalcin da aka yi wa mambobi sama da 7000 da suka shiga jam’iyyar a mazabu da kananan hukumomi da jihohi a jihar Ekiti da kuma zababbun shugabannin jam’iyyar kusan 100,000 a fadin jihohi goma da wasu jihohin biyu da aka bayyana fitar da sanarwar korarsu.