Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufa’i, ya gargadi kungiyar ECOWAS da ta dakatar da shirin amfani da karfin soji kan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.
El-rufa’i ya bayyana cewa, ‘yan Afirka ‘yan uwan juna ne, don haka, yakar daya illa ce ga duk ‘yan Afirka.
El-rufa’i ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin X, wanda aka fi sani da Twitter, inda ya ce, ‘yan kasar Nijar da ‘yan Arewacin Nijeriya abu daya ne.
Tsohon gwamnan ya yi wannan gargadin ne biyo bayan sanarwar da shugabannin tsaro na kungiyar ECOWAS suka yi cewa “ba su da wani zabi illa amfani da karfin soji a kan Jamhuriyar Nijar.”
Kungiyar ECOWAS ba ta jefar da kudurinta ba na amfani da karfin soji domin tunkarar gwamnatin mulkin Janar Abdoulrahamane Tchiani bayan ya hambarar da gwamnatin Dimokuradiyya ta Shugaba Mohamed Bazoum.