Sabon ministan yada labarai da wayar da kan jama’a Muhammad Idris, ya ce, ma’aikatarsa za ta tabbatar da gaskiya a maimakon yin karya wajen kare gwamnati.
Bayan rantsar da shi jiya a Abuja, ministan ya tabbatar da aniyarsa ta gaskiya da gaskiya wajen yada labarai.
Ya ce, gwamnati a shirye ta ke ta dauki alhakin duk wani kuskure da ta yi, kuma za ta yi kokarin yin gyaran da ya dace.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su guji yada labaran karya, inda ya nanata kudurin gwamnati na tabbatar da yada labaran gaskiya ga ‘yan Nijeriya.