• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Birtaniya Ta Gurfanar Da Diezani A Gaban Kotu Kan Zargin Almundahana

by Sadiq
2 years ago
Birtaniya

Birtaniya ta gurfanar da tsohuwar Ministar Man Fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan zargin rashawa lokacin da take Minista.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ’yan sandar kasar sun ce sun maka ta a kotun ne saboda suna zargin ta karbi cin hanci a wasu kwangilolin man fetur da iskar gas.

  • Xi Ya Yi Kira Da A Ingiza Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ta Kudu Zuwa Sabon Matsayi
  • Ba Za Mu Yi Karya Don Kare Gwamnati ba – Ministan Yada Labarai

Diezani, mai shekara 63 a duniya, na daya daga cikin kusoshi a gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.

A zamanin mulkin tsohon Shugaban, Diezani ta rike mukamin Ministar Mai ta Nijeriya daga 2010 zuwa 2015, sannan ta rike matsayin shugabar Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta Duniya (OPEC).

A cewar Shugaban Hukumar Yaki da Laifuffuka ta Birtaniya (NCA), Andy Kelly, “gurfanarwar da aka yi wa Diezani wata somin-tabi ce na wani zuzzurfan bincike na kasa da kasa da aka dade ana yi.”

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

Hukumar dai ta ce ana zargin Diezani da karbar akalla tsabar kudi har Fam din Ingila 100,000 da wasu motoci da hawa jirgin da ba na ’yan kasuwa ba, yin hutun kece raini ita da iyalanta da kuma yin amfani da gidaje masu yawa a birnin Landan.

An kuma zarge ta da nuku-nuku kan wasu kadarori masu tsada da ta mallaka da suka hada da kayan ɗaki da biyan kudin makarantar ‘ya’yanta da kuma wasu sarkoki da kayan ado.

Tun da ta bar mulki a shekara ta 2015, Diezani ta rika fuskantar tuhumar aikata cin hanci da rashawa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86
Da ɗumi-ɗuminsa

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta
Da ɗumi-ɗuminsa

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas
Da ɗumi-ɗuminsa

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

October 22, 2025
Next Post
Sassan Kasa Da Kasa Da Za Su Shiga CIFTIS Na Bana Sun Karu Da Kaso Sama Da 20%

Sassan Kasa Da Kasa Da Za Su Shiga CIFTIS Na Bana Sun Karu Da Kaso Sama Da 20%

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.