Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa mazauna Jihar Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci, ya bayyana cewar, rashin shugabanni na kwarai da ake fama da shi a Nijeriya na daga cikin manyan matsalolin da suke janyo koma baya ga Arewa.
Ya ce, hatta matsalolin tsaron da ake ta fama da su, rashin adilan shugabanni ne ke kara janyo matsalar, sai ya bukaci ‘yan Nijeriya musamman ‘yan Arewa da su yi amfani da lokacin zaben 2023 wajen zaban Shugabanni na kwarai da za su iya kyautata rayuwar al’umma.
“Wannan matsalar sakacin shugabanni ne domin ba mu da Shugabanni wadanda suke kokarin kare ‘yancin ‘yan Arewa ma baki daya, domin da muna da su da wadannan abubuwan ba za su ci gaba da faruwa ba don iyaka yankin arewa ake wannan abun.
“Dan arewa ba shi da ‘yancin zuwa gona ko kasuwa ko hawa hanya, yanzu ka duba tafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja wani tashin hankali ne. Sokoto, Katsina da sauran jihohinmu na arewa ba mu da nutsuwa, wanda gwamnati tana gani ta san halin da ake ciki. Kuma duk Jami’an tsaron nan manya-manyansu ‘yan Arewa ne, hatta shi kansa shugaban kasa dan arewa ne amma duk matsalolin nan a kan arewa ya tsaya.”
Galadanci ya ce, matsalolin tsaro sun haifar da talauci da yunwa a tsakanin jama’a, “Mafita shi ne ‘yan arewa su tsaya su kwaci ‘yancin kansu. PDP ta yi Mulki mun gani, APC ta yi mun gani, yanzu ‘yan Nijeriya su ne za su yi wa kansu zabi wanda za su samu mafita a wannan lokacin.”
Ya ce tabbas Nijeriya babu shugabanni nagari, “abun kunya yara da suke karatu a jami’o’i yau watansu nawa a gida? Ba wanda ya fito ya yi magana domin ‘ya’yan shugabannin ba a Nijeriya suke karatu ba.”
“Kullum fa dan arewa shine aka bari cikin damuwa, ka bar Arewa ka zo sana’a a Kudu ma a kama ka a kai ka kurkuku ba ka yi laifi ba, ba wani abu ba wanda zai bi kadin ka. Muna zaune ne kawai zaman dole ba yadda za mu yi.” In ji shi.
Ya yi kira ga ‘yan arewa su tabbatar da shugabanni nagari kadai ne suka zaba a 2023 domin fita daga wannan kangi.