A sakamakon fada da ta kaure a tsakanin mambobin Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, Boko Haram da Islamic State of West African Province (ISWAP) a kalla mutum 41 ne daga cikin mambobin bangarorin biyu suka rasa rayukansu sakamakon fadan.
Daga cikin wadanda suka mutun har da kwamandojin Boko Haram bayan wata rashin jituwa ta barke a tsakaninsu a ranar Laraba a Kukawa da ke jihar Borno.
- Ci Gaban Dangantakar Sin Da Afirka Ya Kama Hanyar Bunkasa Cikin Sauri
- Hatsarin Kwale-kwale Ya Hallaka Rayukan Mutum 12 A Nasarawa, Majalisa Ta Jajanta
An tattaro cewa mambobin ISWAP wadanda suka zo a kan jiragen ruwa sun farmaki bangaren ‘yan boko Haram da Bakoura Buduma ke jagoranta a hanyar Duguri da ke karamar hukumar Kulawa.
Majiyoyi masu karfi da suke da masaniya kan artabun, sun shaida wa Zagazola Makama, mai sharhin lamuran tsaro a yankin Lake Chad, cewa artabun ta janyo sun kashe junansu har mutum 41 ciki har da kwamandoji.
Majiyar ta ce ISWAP sun yi jina-jina wa ‘yan Boko Haram har da kwamandoji da suka kashe.
Majiyar ta jero wasu daga cikin kwamandoji da Modu Kayi, Abbah Musa, Isa Muhammed, Ibrahim Ali, Kanai Zakariya and Bula Salam, Isuhu Alhaji Umaru, Dogo Salman da Abdulrahman Malam Musa gami da wasu.
Rikici tsakanin mambobin ISWAP da Boko Haram dai ya zama ruwan dare.
ISWAP dai yanzu ta samu wani da yake taimaka musu riskan ‘yan Boko Haram wato Abou Idris da ya canza sheka daga Boko Haram ya shiga ayarin ISWAP hakan ya sa yake yakan tsohowar kungiyarsa.