Biyo bayan taron addu’a darikar Kwankwasiyya a Kano ta yi don samun zaman lafiya da kuma neman nasara a kotun sauraren kararrakin zabe, shugabannin jam’iyyar APC na Kano karkashin jagorancin Abdullahi Abbas sun umarci al’ummar Kano da ‘ya’yanta na mazabun 484 da ke Kano da su gudanar da tasu addu’a a ranar Litinin.
Wata majiya mai tushe ta bayyana NIGERIAN TRACKER shirin gudanar da taron addu’ar.
- Somaliya Ta Haramta TikTok Da Telegram Don Dakile Yaduwar Batsa
- Gwamnatin Kano Ta Gudanar Da Sallar Alkunut Domin Samun Nasarar Shari’ar Da Ake Yi A Kotu
Majiyar ta bayyana cewa shugabannin jam’iyyar APC na Kano sun kuduri aniyar gudanar da addu’o’i da azumi a ranar Litinin, sakamakon kalubalen da gwamnatin NNPP ta Kano ta gindaya, wanda ya shafi kasuwancin mutane, musamman ta hanyar rushe-rushe.
Shugaban jam’iyyar Abdullahi Abbas ya ce manufar addu’ar ita ce a roki Allah Madaukakin Sarki da ya kawo dauki da kuma daukaka darajar Kano.
Bugu da kari, majiyar ta jaddada cewa ‘ya’yan jam’iyyar APC da dimbin magoya bayansu sun yi maraba da wannan umarni, suna dakon ranar da aka ware.
Majiyar ta ce shugaban jam’iyyar APC ya bukaci jama’a da su yi wa APC addu’ar samun nasara a kotun sauraren kararrakin zaben gwamna.