A jiya Asabar ne kasar Sin ta cimma nasarar bunkasa fasahar sarrafa dumin makamashin nukiliya, domin samar da haske makamancin na rana, inda a karon farko, hasken da aka samar ta sinadarin Huanliu-3 ko HL-3, cikin da’irar kwallon ranar bil adama, ya kai “amperes” miliyan daya.
A cewar hukumar lura da makamashin nukiliya ta Sin ko CNNC, nasarar da aka samu ta wannan karo, ta sanya Sin din wucewa gaba, a fannin cin gajiyar wannan fasaha a duniya, matakin da ya kai Sin din muhimmin matsayin ci gaba a fasahar sarrafa makamashin nukiliya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)