Farfesa Bem Angwe, dan takarar gwamna a jam’iyyar (NNPP) a Jihar Benue a zaben 2023, ya sauya sheka daga jam’iyyar.
Ficewar ta Angwe na kunshe ne a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu da ya aika wa shugaban Jam’iyyar NNPP na mazabar Mbatyu a karamar hukumar Gboko a jihar Benue.
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohowar Shugaban Kotun Gargajiya A Benue
- EFCC Ta Damke ‘Yan Damfarar Intanet 17 A Benue
Angwe, shi ne tsohon mashawarcin shugaban Jam’iyyar na kasa kan harkokin shari’a kafin fitarsa daga NNPP
gabanin taron kwamitin zartaswa na NNPP (NEC) wanda aka shirya gudanarwa a ranar 29 ga Agusta, 2023.
“A sakamakon yin shawara da dattawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da na yi da Jama’a jihar Binuwai na fice daga jam’iyyar;
“Don kaucewa shakku, na sanar da sanarwar ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa ga shugaban kwamitin gudanarwa na mazabar Mbatyu NNPP a karamar hukumar Gboko ta jihar Benue.”
Tsohon dan takarar gwamnan ya godewa jiga-jigan jam’iyyar a mazaba, Kananan Hukumomi da na Jiha bisa goyon bayan da suka bayar.
“Ina kuma mika godiya ta ga ’ya’yan jam’iyyata da magoya bayana da kuma dukkan masoyana a fadin jihar Binuwai da ma Nijeriya baki-daya bisa irin goyon bayan da suka ba ni a lokacin yakin neman zabena na gwamna.
“Ina jinjina wa da irin jajircewa da duk wadanda suka yi imani da ni da kuma suka yi kokarin tafiya tare da ni har zuwa karshen wannan lokaci.
“Ina tabbatar muku da cewa a muna tare, kuma kowane lokaci zan ci gaba da tafiya tare da ku a cikin harkokina na gaba,” in ji shi.