Yau Talata ne aka shirya taron tattauna kan tsaron Sin da Afirka bisa taken “Tabbatar da shawarar tsaron duniya, da kuma karfafa hadin gwiwar Sin da Afirka” karo na uku a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan tsaron kasar Li Shangfu ya halarci taron tare kuma da gabatar da wani mihimmin jawabi.
Bayan taron bi da bi ne minista Li ya gana da manyan jami’an hukumomin taron kasa na kasashen Senegal, da Comoros, da Congo (Brazzaville), da Kamaru, da Ghana, da Zambiya, da Sudan ta Kudu, da Gambiya, da Mauritania, da Uganda, da jami’in hukumar kungiyar AU mai kula da harkokin siyasa da kwanciyar hankali. (Mai fassara: Jamila)