Ministan kula da muhalli da halittu na kasar Sin, Huang Runqiu ya bayyana a birnin Beijing cewa, kasar Sin tana sabunta dabarunta da tsare-tsare kan ayyukan kiyaye mabambantan halittu na kasa (NBSAP) a wani bangare na kokarin aiwatar da tsarin kiyaye mabambantan halittu na Kunming-Montreal na duniya.
Huang ya bayyana hakan ne jiya Talata, a yayin taron shekara-shekara na majalisar hadin gwiwar kasa da kasa kan muhalli da raya kasa na shekarar 2023.
A cewar Huang, tsarin ya kasance daya daga cikin nasarorin da aka cimma a shekarar da ta gabata, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, ciki har da wadanda kasar Sin ta yi, yayin da ta jagoranci taro na 15 na sassan da suka sanya hannu kan yarjejeniya kan kare mabambantan halittu
Don haka, ya yi kira ga dukkan bangarorin da su hanzarta yi wa tsare-tsarensu na NBSAP kwaskwarima kamar yadda aka tsara, tare da kara samar da albarkatu don dakile asarar halittu masu rai. Ya kuma bukaci a kara yin hadin gwiwa kan aiwatar da tsarin yadda ya kamata, da samar da sabon yanayi cikin hadin gwiwa a fannin gudanar da ayyukan kare mabambantan halittu a duniya.(Ibrahim)