A wannan makon ne galibin zababbun gwamnonin jihohin kasar nan ke cika kwana 100 a kan karagar mulki, ciki har da sabbin da suka shigo a karon farko da kuma wadanda suke a kan wa’adi na biyu.
Ganin muhimmancin kwana 100 a kowacce gwamnatin dimokradiyya, musamman a yanzu da al’umnma ke fama da matsaloli a bangaren tsaro, tattalin arziki da zamantakewar rayuwa gaba daya, ana iya fahimtar inda gwamnatin kowace jiha ta nufa bisa irin ayyukan ci gaba da ta gabatar ko ta aza tubalin yi cikin kwana 100.
- Ana Zura Ido Kan Yadda Amurka Za Ta Ki Raba-gari Da Kasar Sin
- Sakaci: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Asibitin Hasiya Bayero
Wakilanmu sun yi nazarin halin da ake ciki a wasu Jihohin Arewacin Nijeriya, musamman sabbin gwamnonin da aka samu wadanda suka hau karagar mulki, saboda dokin da jama’a suke yi a kansu da kuma irin kamun ludayinsu.
Sakkwato
Gwamna Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC, wanda ya yi galaba a kan Sa’idu Umar na jam’iyyar PDP bayan karewar wa’adin zangon mulki biyu na Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya gaji gawurtacciyar matsalar tsaro wadda ta addabi al’ummar Gabacin Sakkwato ba tare da hobbasar kwazon Gwamnatin Tarayya na shawo kan matsalar ba.
Jim kadan da shigar sa ofis, Gwamna Aliyu ya gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro tare da alwashin daukar kwararan matakan da suka wajaba, domin ganin al’ummar yankin sun ci gaba da bacci da idanu biyu; akasin halin hare- hare, garkuwa da mutane da kisan gillar da ‘yan ta’adda ke yi musu ba kakkautawa. Daga bisani, Gwamnan ya yi ganawar musamman da Shugaban Rundunar Tsaro, Manjo Janar Chirstopher Musa da zummar kakkabe ayyukan ta’addanci a fadin Jihar baki-daya.
A cikin kwana 100, Gwamnan ya magance matsalolin da jami’an tsaron ke fuskanta da suka hada da biyan bashin alawus na wata biyar da alkawarin duba matsalar rashin ingantattun motoci da suke fama da shi da kuma aminta da dukkanin bukatar da suka gabatar, wanda hakan zai inganta ayyukansu.
Gwamnatin Sakkwato, wadda tuni ta nada ‘Yan Majalisar Zartaswar Gwamnatin Jiha da Mashawartan Gwamna na Musamman da Kantomomin Kananan Hukumomi tare da wasu muhimman mukamai, baya ga biyan albashi a cikin lokaci, tuni ta fara aiwatar da ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma ta hanyar shimfida hanyoyin motoci a wasu zababbun unguwanni tare da ci gaba da kokarin kammala gadar sama a Rijiyar Doruwa, wadda Gwamnatin Tambuwal ta bayar da kwangilar ginawa a kan naira biliyan 3.5.
Haka zalika, gwamnatin ta aiwatar da kawata tagwayen babbar hanyar Fadar Gwamnati da ado na musamman. Sai dai tuni jam’iyyar PDP a Jihar ta nuna rashin dacewar bayar da kwangilolin hanyoyin ba tare da amincewar Majalisar Zartaswar Jihar ba, wadda a lokacin ba a kafa ba. Jam’iyyar ta ce ko kadan ba a bi doka da ka’ida ba; wajen bayar da ayyukan wadanda kuma ta ce ba a bayyana adadin kudin aikin da kuma ‘yan kwangila ba.
Jihar Sakkwato, wadda ke fama da yawaitar shara a mafi yawan wurare, ta kafa kwamiti na musamman a karkashin jagorancin fitaccen dan siyasa, Alhaji Ummarun Kwabo (Jarman Sakkwato) domin tsaftace Birnin Sakkwaton, aikin da tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
Bugu da kari, matakan da gwamnati ta dauka na magance matsalar wuta a Asibitin Kwararru ta jiha da kokarin magance matsalar ruwan sha da dawowa da kuma biyan tallafin wata- wata na marasa galihu; duka al’ummar jihar sun yaba.
A siyasance kuma, tuni sabuwar Gwamnatin Sakkwato ta fara binciken Gwamnatin Tambuwal, wadda suke da zazzafar adawa ta hanyar kafa hukumar bincike da zummar alhakin binciken gwanjon motoci da gidaje da Tambuwal ya yi kafin ya bar mulki tare da filayen da gwamnatinsa ta raba kyauta da kuma gidajen da aka sayar. Haka nan kuma, gwamnatin ta soke dukkanin mukaman da Tambuwal ya nada bayan zabe tare da dakatar da dukkanin Sarakunan Gargajiya da tsohuwar gwamnatin ta nada a karshen mulkinta.
Har wa yau, tuni Jam’iyyar PDP ta bayyana wannan bincike a matsayin bita- da –kulli, don tozarta jami’anta. A cewar Kakakin Jam’iyyar, Hassan Sahabi Sanyinnawal, an gudanar da gwanjon ne a bisa ka’ida ba tare da saba wa doka ba, sannan su kansu jigogin APC a jihar sun amfana da wannan gwanjo a baya. Sai dai Kakakin Gwamnatin ta Sakkwato, Abubakar Bawa ya ce babu nufin tozartawa a wannan bincike, illa a bincika idan an bi ka’ida kamar yadda doka ta tanada ko kuma akasin hakan.
Kano
Siyasar Jihar Kano ta sha banban da siyasar sauran Jihohin Kasar nan, musamman ganin irin salon siyasar bai wuce hannun karba hannun mayarwa ba. Domin idan za a iya tuna Shekarar 1979 da Gwamna Abubakar Rimi ya dare mulkin Kano, wa’adin Shekara hudu kawai ya samu, daga nan abokin adawarsa Sabo Bakin Zuwo ya karbe kujerar, hakan ce ta faru a shekara ta 1999, inda Kwankwaso ya lashe zaben Gwamna, amma shi ma shekara hudu kacal ya samu a kan mulki, sai abokin hamayyarsa na Jam’iyyar ANPP; Malam Ibrahim Shekarau ya kwace mulkin, wanda shi ne gwamna na farko da ya yi nasarar sake cin zango na biyu a kan karagar mulki, amma shi ma daga karshe Kwankwason ya sake dawowa a shekara ta 2011 ya karbe mulkin daga hannun jam’iyya mai mulki, a wancan lokaci ta ANPP.
Bayan da Kwankwaso ya karasa, cikin shekaru hudunsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, sai ya mika wa Mataimakinsa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ma ya yi sa’ar yin zango biyu a kan karagar mulkin, daga nan kuma sai NNPP wadda Abba Kabir Yusif ya tsaya wa takara ya kayar da jam’iyya mai mulki ta APC, wanda yanzu haka yake cika Kwana 100 a kan karagar mulkin Jihar Kano.
Tun bayan rantsar da shi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana manufofin gwamnatinsa na cika alkawuran da suka dauka a lokacin yakin nemnan zabe, wadanda suka hada da kwato dukkanin wasu filaye ko kadarar da gwamnatin da ta gabata da ake zargin yin watandarsa. Sai kuma shirin gwamnatin tasa na sake dawo da tsarin tura ‘ya’yan talakawa zuwa kasashen waje domin samun digiri har da digirgir, wanda yanzu haka dalibai 501 ke jiran tashinsu zuwa makarantu daban- daban, domin ci gaba da karatu a kasashen na waje, ga Kuma shirin nan nasa na Aurar da Zawarawa, wanda a halin yanzu aka sauya wa suna da Auren ‘yar Gata.
Shi ma yanzu haka, aikin ya yi nisa na aurar da wadannan Zawarawa kimanin 1,800, wadanda aka warewa kudin lakadan ba ajalan ba; Naira Miliyon 840,000,000.00, sai kuma sake farfado da Makarantun SAS a fadin Kananan Hukumomin Jihar Kano 44.
Gwamnatin Abba Kabir Yusif, ta bayyana tare da zartar da shirin dawo da ladabin Ma’aikatan Gwamnati, sake dawo da Asibitin Yara na Hasiya Bayero da a baya ake zargin sayar da shi.
Gwamna Abba Kabir, ya kuma ayyana biyan daukacin kudaden ‘yan fansho, komawa aikin matatar ruwa da ke Tamburawa domin wadata Kano da ruwan Sha, biya wa daliban Jihar Kano kudin Jarrabawar NECO da kuma sake ginin wasu shataletalen da ke kwaryar birnin jihar.
Bugu da kari, babban abin da ke daukar hankalin jama’a shi ne, barazanar da Gwamna Abba Kabir Yusif ya yi wa Kwamishinoninsa a lokacin da yake rantsar da su, inda ya sanar da cewa zai sa wa ayyukan Kwamishinonin ido cikin watanni shida na farko, wanda duk ya gaza cimma abin da ake bukata ya tabbatar da cewa sallamar sa gwamnan zai yi. Sai kuma sake fasalin yadda ake tattara harajin Jihar ta Kano, samun nasarar sulhunta sabanin da ke wakana tsakanin Hukumar Al’adu ta Jihar Kano da kuma Hukumar Tace Finafinai. Dawo da ciyar da daliban makarantun firamare tare da dinka musu kayan makaranta.
Ta fuskar tallafawa mata da matasa da hanyoyin dogaro da kai, Gwamnatin Abba cikin kwanakin 100 ta waiwayi shirin nan na CRC, wanda ake raba wa mata 100 daga kowacce Karamar Hukuma jarin naira dubu goma-goma, sai kuma batun Makarantar Koyon Sana’o’u, ita ma tuni wannan gwamnati ta sake dawowa kanta gadan-gadan.
Babban kalubalen da Gwamnatin ta Injiniya Abba Kabir Yusif ke fuskanta, bai wuce rusau da ta gudanar ba, wanda ko shakka babu wannan ya taba zukatan ‘yan Kasuwar da suke ganin sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar gwamnatin tasa. Haka nan, batun korarar wasu ma’aikata da ake zargin gwamnatin da ta gabata ta dauke su ba bisa ka’ida ba. Amma dai kamar yadda kowa ya sani, dukkan abubuwan nan jama’a sun kwana da sanin su, domin tun yana yakin neman zabe ya yi ikrari tare da alkawarin farawa da su da zarar ya samu nasarar cin zabe, sannan ba don Kotu ta dakatar da aikin ba; da tuni aikin gama ya riga ya gama.
Zamfara
Cikin manyan kalubalen da sabon Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal ya fuskanta a yayin da ya karbi ragamar jagorancin Jihar Zamfara ya hada da matsalar tsaro, wadda ta ki ci ta ki cinyewa.
Cikin matakan da gwamnan ya dauka a cikin kwana 100 na farkon mulkinsa, sun hada da ziyartar Shugabannin Rundunonin TSaro tare da karfafa musu gwiwa ta hanyar samar musu da cikakken kayan aiki. Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci mai ba wa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribado, ya kuma nemi hadin kan shugabannin al’umma da Sarakunan Gargajiya, saboda muhimmancinsu a tsarin tafiyar da al’umma da zamantakewa, a cewarsa su ne suka fi kusa da al’umma, don haka dole a tafi tare da su.
A watan Agustan 2023 ne kuma ya kaddamar da fara aikin yin sabbin hanyoyi a Birnin Gusau, duk a cikin shirinsa na sabunta biranai.
Sashen farko na wannan aikin za a fara ne da yin hanyoyi guda hudu masu tsawon kilomita 3.1, wanda kuma za su hada da manyan kwalbati da sauran makamantansu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa, an yi bikin kaddamarwa ne a titin Gidan Sambo, daura da ofishin ‘yansanda da ke Gusau.
Ya kara da cewa, wannan aiki na hanyoyi yana daga cikin alkawuran da Gwamna Dauda ya dauka a lokacin yakin neman zaɓensa; cewa zai sabunta biranai ta hanyar gina ingantattun hanyoyi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A wurin bikin kaddamarwar, Gwamna Lawal ya jaddada aniyarsa ta sabunta biranai a fadin Jihar Zamfara, lamarin da aka rasa a gwamnatocin baya.
“Sashen farko na aikin, zai zagaya shatale-talen Bello Barau zuwa Hanyar Babban Ofishin ‘yansanda zuwa gidan gwamnati, zuwa Kwanar ‘Yan Keke, zuwa Fadar Sarki, zuwa Tankin Ruwa.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi imanin cewa, idan aka samar da hanyoyi masu inganci tare da bunkasa biranai, ko shakka babu zai taimaka wajen kawo wa jihar masu zuba hannun jari.
“Haka nan kuma, Gwamna Dauda ya nemi alfarmar jama’ar Gusau da su yi hakuri da duk wata takura da aikin zai haifar, saboda za a mori alfanunsa nan gaba kadan masu yawa.”
Kaduna:
A yayin da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ke shafe kwana 100 a kan karagar Shugabancin Jihar, alamu sun nuna cewa, akwai ci gaba ta fuskar magance matsalar tsaro a jihar; duk kuwa da cewa akwai sauran rina a kaba.
Har ila yau, manyan abubuwan ci gaba da Gwamnatin Uba Sani ta aiwatar a cikin kwana 100, mafi jan hankali a cikinsu su ne kaddamar da aikin gina rukunin gidaje 5,000 ga talakawa da kuma rage kudin karatu a manyan makarantun jihar.
Gwamnatin ta rage kudin karatu a Jami’ar Jihar Kaduna daga 150,000 zuwa 105. Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli daga 100,000 zuwa 50,000, Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya daga 75,000 zuwa 37,500, sai kuma Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi da aka rage kudin daga 100,000 zuwa 70,000, kana Kwalejin Horar da Malaman Jinya da aka rage kudin karatunta daga 100,000 zuwa 70,000.
Dangane da sha’anin tsaro, wakilinmu ya ji ta bakin Mista Samson Auta, wanda ya fito daga Kudancin Kaduna; kuma har ila yau jagoran Kungiyar Dakile Tashin Hankali a Cikin Al’umma ta CMMRC, ya ce an samu raguwar kai wa al’umma hare-hare cikin watanni uku da suka wuce, musamman a Kudancin Kaduna.
Samson ya kara da cewa, maiyuwa an samu raguwar kai hare-haren ne, saboda kokarin sojoji da sauran hukumomin tsaro da kuma kokarin kungiyoyi masu zaman kansu na sasanta al’ummar da ke zaman doya da manja a tsakaninsu da juna.
Sai dai, ya ce, ana ci gaba da samun ‘yan hare-haren, musamman na masu yin garkuwa da mutane, inda suke sace matafiyan da suka biyo babbar hanyar Karamar Hukumar Kajuru tare da yin kisa a wasu lokutan.
Shi kuwa wani mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum, Alhaji Musa Bala, ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, gwamnatin a watanni uku da suka wuce, ta yi kokarin inganta tsaro da baiwa matasa damar komawa makaranta ta hanyar rage kudin karatu, “domin duk wanda ba ya zuwa makaranta, Allah ne kadai ya san irin halin da zai iya shiga na aikata ayyukan da ba su dace ba.”
Haka zalika ya ce, Gwamna Uba Sani ya yi kokari wajen kawo masu zuba jari daga Katar, domin gina gidaje da bunkasa fannin kiwon kaji, wanda hakan zai kara samar da ayyukan yi da kawar da tunanin matasa daga shiga halin rashin tsaro.
Shi ma mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum, kuma Shugaban Kungiyar Manoman Masara na yankin Arewa maso yamma, Alhaji Adamu Mohammed Makarfi ya ce, ya zuwa yanzu “mun godewa Allah domin kuwa ana samun sauki sosai, musamman ta fuskar rage kai wa manoma hare-hare da ake yi a wasu guraren.”
A cewar ta Makarfi, amma gaskiyar magana abin damuwa a wasu bangarorin guda biyu, musamman a Kananan Hukomomin Birinin Gwari da Giwa, har yanzu ana ci gaba da samun koke-koken kai wannan hare-hare.
Daga bangaren jami’yyar adawa kuwa, Shugaban Jami’yyar ADC reshen Jihar Hon. Ahmed Tijjani Mustapha, ya yaba da abubuwan da Gwamna Uba Sani ya yi a bangaren ilimi, domin yara su samu ingantaccen ilimi kyauta tun daga matakin Firamare har zuwa Sakandire.
A wani bangaren kuma, Gwamna Uba Sani a kwanan baya ya amince da a kebe ware 15 a cikin kasafin kudi na shekara-shekara na jihar, domin kara bunkasa fannin kiwon lafiya.
Neja
A daidai lokacin da Gwamnatin Neja, karkashin sabon gwamnan jihar, Rt. Hon. Umar Mohammed Bago ke cika kwana 100, jama’a da dama sun zura idanu don ganin kawo karshen matsalar tsaron da ya kai ga al’ummomi da dama barin gidajensu da gonakinsu, sakamakon tsoron yawaitar hare-haren da ‘yan bindiga ke kai musu, musamman a yankunan karkara da abin ya fi shafa a bangarorin yankin Neja ta gabas da Arewa.
Duk da kokarin da take yin a matsalolin da ta gada daga gwamnatin da shude, an samu nasara a wasu yankunan kamar matsalar sara suka da aka yi tanadi na musamman na kafa Rundunar Tsaro, wadda ta himmatu musamman a kan kwaryar garin Minna; inda gwamnatin ta sayo motoci don karfafa guiwar rundunar akalla guda ashirin, wanda aka damka su ga jami’an ‘yansanda, Rundunar Yaki da hana fatauci da shan miyagun kwayoyi, jami’an tsaron fararen hula da ‘yan sinitiri.
Lamarin ya yi wa al’ummar cikin garin Minnan dadi, musamman yadda rundunar da zage damtse ba dare ba rana, lungu da sakon kwaryar cikin garin na Minna na ganin bayan ‘yan sara suka cikin kwaryar Minna da ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyin jama’a da matasan kan aiwatar a lokacin hare-harensu.
Sai dai lokacin da ake ganin jami’an tsaron bisa goyon bayan gwamnatin, sun samu damar karya lagon sara sukar, a bangaren ‘yan fashin daji da ke kai hare hare ga mutanen karkara kuwa, abin ya dauki sabon salo, inda ‘yan bindigar ke kai sumame ga mutanen karkarar na dauki dai-dai.
Yanayin noma ga mutanen karkara kuwa, duk da cewa ‘yan bindigar ba su cika shiga garuruwan karkara ba, rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu ‘yan bindigar na da iko da wasu yankunan, musamman duba da irin harajin da suke kakaba wa mutanen karkarar manoma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, tun a shekarun baya da ‘yan bindigar suka fara sanya harajin; abin kullum gaba yake sake yi, misali kauyen Dusai da Gulbin Boka da ke Karamar Hukumar Mariga, a bayan nan sun shiga sahun ‘yan harajin da ‘yan bindigar suka kakabawa. Dusai dai ana neman naira miliyan tara a hannunsu kafin su samu damar mayar da hankali kan gonakinsu, Gulbin Boka kuwa, wani mazauni garin ya ce ‘yan bindigar sun umarci su biya naira miliyan arba’in, wanda hakan ya tilasta wa manoma da dama yin hijira domin canja matsuguni, bayan mutanenmu da dama da ke hannun ‘yan bindigar suna garkuwa da su.
Hon. Aminu Musa Bobi, Shugaban Jam’iyyar APC na riko a Jihar Neja, wanda ya taba zama mamba a kwamitin tsaro da gwamnatin da ta shude ta kafa, musamman a yankin Masarautar Kontagora, wanda kuma ya taba fadawa komar ‘yan bindigar, cewa ya yi; “maganar gaskiya gwamnati da jami’an tsaro na bakin kokarinsu kan lamarin, wannan wani iftila’i ne da Allah ya jarabce mu da shi. Babban abin da ya kamata jama’a su sani shi ne, bai wa gwamnati da jami’an tsaro hadin kai tare da komawa ga Allah na neman mafita a kan wannan lamari.”
Tun bayan hawan gwamnatin kan wannan mulki, jama’a ke tsammanin kafin kwana dari na mulkin Bago, an yi nisa da wasu ayyukan raya kasa, musamman ma batun kammala aikin hanyar Minna zuwa Bida, hanyar Kontagora zuwa Bida da wasu ayyukan Gwamnatin Tarayya da ya shafi hanyar Bida-Agaie, Lapai zuwa Lambata da hanyar Suleja da aka fara tun mulkin Jonathan.
Zuwa yanzu dai, kusan wadannan da gwamnatin ta sha alwashin idan ta kammala daidaituwa za ta dora dan ba a kai, akwai alamar ayar tambaya a kai, musamman dangane da rahotanni da ke yawo na samun makudan kudaden da aka ce gwamnatin ta yi da har yanzu ba ta kammala natsuwar da zai baiwa jama’a kwarin guiwa ba.
Wani abin farin ciki da kafa tarihin da gwamnatin ta yi cikin kwanakinta kalilan shi ne, bai wa mata dari da talatin da daya mukaman siyasa, bisa ikirarinta na cika alkawarin da ta yi musu lokacin yakin neman zabe.
Haka nan gwamnatin ta yi rawar gani wajen kafa sabuwar Ma’aikatar kula da Harkokin Fulani, irin ta ta farko a tarihin Arewacin wannan kasa, wanda damka Ma’aikatar a hannun kungiyoyin Fulani, inda suka ba da kwamishinan da zai jagoranci Ma’aikatar, wanda cikakken Bafilatani ne.
Dangane da muhimman ayyuka kuwa, Gwamna Umar Mohammed Bago, ya ce kwanakinsa dari a kan kujerar Gwamnatin Jihar, zai mayar da hankali ne a kan tsara kudurce-kudurcensa na shekaru hudu a kan mulkin jihar, inda zuwa yanzu Ma’aikatar Ayyuka ta himmatu wajen tsara taswirar ayyukan hanyoyi dari biya da hamsin da daya da gwamnatin ke kudurin farawa da kammala su a kankanin lokaci.
Hususan dai, a cikin kwanaki darin na mulkin Bago, babu wani abin da jama’a suka fi shauki kamar kawo karshen matsalar tsaro, samar da guraben ayyuka ga matasa da gwamnatin ta ce za ta fi mayar da hankali a kansu, musamman bangaren noma da samar da ayyuka da abinci da kuma tsaron kasa.
Filato
A jihar Filato kuwa, kamar sauran sabbin gwamnoni, Gwamna Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP, a gabar cika kwana 100 a kan karagar mulki, bincike ya nuna cewa ya taka rawa a wasu bangarori. Kazalika, a wasu bangarorin kuma ya gaza. Tun lokacin da gwamnan ya hau kan mulki, bai yi fashin biyan albashin ma’aikata ba, sai dai wasu hakkoki kamar kudaden hutu da na fansho har zuwa yanzu bai biya ba, kazalika an samu matsalar tsaro tun a farko-farkon gwamnatinsa.
Koda-yake a kwanakin baya, Gwamna Caleb ya ce, gwamnatin baya ta Simon Lalong ta gadar masa da bashin albashi na kimanin naira biliyan 11 da bai biya ma’aikata ba.
Shi dai sabon gwamnan, Caleb Mutfwang, a lokacin amsar mulki, ya yi alkawarin hada kan al’ummar jihar ne, sannan kuma ya gargadi masu kunna wutar rikici da raba kawukan jama’a da cewa, daga yanzu su daina domin shi kam ba zai lamunci hakan ba.
Sai dai za a iya cewa, gargadin nasa bai yi tasiri ba, domin kuwa an samu kashe-kashe a cikin kwanaki 100 na mulkinsa. A fadin gwamnan, ya kamata ne kowa ya ba da gudunmawarsa wajen kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ba tarwatsa kawuna ba.
Sannan, ya koka kan yadda gwamnatin da ya amshi mulki a hannunta ta gadar wa gwamnatinsa tulin basuka da suka haura sama da biliyan N200.
“Ba za mu tozarta kowa ba, kuma ba za mu zauna muna sukar juna ba, za mu yi zurfin tunani mu dauki matakin gyaran abubuwan da muka gada yau, amma muna
bukatar mu yi wasu tulin tambayoyi, saboda muna bukatar mu yi aiki tukuru mu kafa tarihi wajen kyautata mulkinmu,” ya shaida.
Bisa bayanan da kungiyar ci gaban kabilar Mwaghabul (MDA) da kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta MACBAN suka gabatar, sama da mazauna kauyukan Mangu da wasu Fulani sama da 200 ne aka kashe a tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin 2023, lamarin da ke kara jefa jama’a cikin zaman dar-dar.
Kodayake, a wata tattaunawa mai magana da yawun gwamnan jihar Filato Gyan Bere, ya ce har yanzu gwamnati ba ta samu rahoton yawan mutanen da aka kashe a rikicin na baya-bayan nan ba.
Shugaban kungiyar ci gaban Mwaghabul (MDA), Cif Joseph Gwankat, ya ce, “Mun fito ne domin mu shaida muku hakikanin abubuwan da suke faruwa da muhallanmu. Wasu ‘yan ta’adda na kai hare-hare a Mwaghabul da wasu sassan Karamar Hukumar Mangu.”
“Hare-haren da Fulanin suke kawo mana ya fara ne tun a watan Afrilu har zuwa yanzu, da farko lamuran sun fara da garkuwa da mutane, lalata gonaki da wasu matsaloli daga baya lamarin ya zama kaddamar da hare-hare.”
Sai dai kuma, Shugaban Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), Nuru Abdullahi a jihar, ya karyata cewa Fulani ne ke janyo wadanan matsaloli, inda ya yi zargin cewa, su ma ana kashe musu mambobi haka siddan.
A kwanakin nan, gwamnan ya sanar da shirin gwamnatinsa na yin hadaka da masu abokan jere, domin kyautata harkokin kiwon lafiya. Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta yi sake da kiwon lafiyar al’ummar jihar ba.
Daga cikin abubuwan da gwamnan ya samu cimmawa a wannan kwanaki, sun hada da samun nasarar nada sabbin kwamishinonin da za su taimaka masa wajen gudanar da harkokin mulkin jihar. A kuma ranar 4 ga watan Agustan 2023 ne, gwamnan ya rantsar da kwamishinonin nasa.
Kuma gwamnan na Filato, Barista Caleb Manasseh Mutfwan ya shirya wa jami’an gwamnatinsa taron kara wa juna sani, domin sanin makamar aiki da inda aka dosa, ba wai yin aiki ido a rufe ba.
A wani babban matakin shawo kan rikici a wasu yankunan Filato, gwamnan jihar, ya ba da umarnin samar da filin noma mai girman hekta 900, a sassan Kananan Hukumomi uku Mangu, Barkin Ladi da Riyom da ke jihar, domin dakile yawaitar fadace-fadacen da ake samu a yankunan.
Wannan mataki na ware filin noma, za a iya cewa wani kokari ne sosai da gwamnan ya yi domin kawo karshen rikice-rikicen da ake yawan samu a sassan wuraren.
A wani mataki na garanbawul ga harkar ilimi, Gwamnan Jihar Filato, ya sha alwashin cewa zai kafa hukumar kula da manyan makarantun sakandari, domin kara samar da kula ga sashin ilimi.
Dukkanninsu a cikin kwana 100, gwamnan ya yi alkawarin cewa zai samar da takin zamani masu tarin yawa da kayan noma da kuma tiraktoci a nan kusa, domin kyautata harkokin noma a fadin jihar.
Har-ila-yau, gwamna Caleb, ya yi alkawarin maida ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu na asali, wadanda suka yi kaura daga muhallansu sakamakon matsalolin tsaro.
Duk a cikin kokarin gwamnatin tasa na kyautata alaka da abokan jere, gwamnan ya kaddamar da sufurin jirgi daga Abuja zuwa Jos kai tsaye, domin kyautatawa da fadada harkokin sufuri. Kamfanin BalueJetAirline shi ne ya cimma yarjejeniya da Gwamnatin Jihar, domin fara jigilar.
A baya-bayan nan kuma, Gwamnan Filato Caleb, ya bukaci hadin kan Gwamnatin Kasar Kanada, a bangarorin gine-gine, harkokin noma, daidaiton jinsi da sauran bangarorin kyautata rayuwa.
Benuwai
A Jihar Benuwai kuwa, Gwamna Hyacinth Alia, a cikin kwanakinsa 100 a mulki ya samu nasarar nada kwamishinoni 17 da masu ba shi shawara 23. Domin bunkasa abinci, Gwamnan Benue ya nemi goyon bayan gwamnatin tarayya. Kana a wani matakin fara gwamnati da Bismilla a cikin kwanakinsa 100, ya kaddamar aikin shimfida titina na sama da naira biliyan shida (6b), hanyoyin da za a gina din guda 16 a cikin garin Makurdi za haura sama da kilomita 15.39.
A cewar gwamnan, aikin zai lakume sama da bilyan shida a yayin gudanar da shi cikin watanni 11 kacal.
Haka zalika, gwamnan cikin wannan kwanaki nasa, ya kafa kwamitin da za su sanya idanu a kan dakile yaduwar cutuka a fadin jihar.
A kokarin Gwamna na kyautata aikin gwamnati, cikin kwana 100, ya samu nasarar bankado ma’aikatan boge 2,500 da suke amsar albashi ta haramtatun hanyoyi. Haka zalika, an samu wannan nasarar ne a aikin bincike da tantance ma’aikatan karo na farko da gwamnatin ta yi.
Gwamnan ya sanar da aniyarsa ta tsarkake sashin biyan albashin ya na mai cewa, ba zai bari wasu na lalata tsarin aikin gwamnati ba. Matakin a cewar gwamnan, ya taimaka wajen samun rarar naira biliyan 1.2.
Bugu da kari Gwamna Alia, ya kafa kwamitin da zai binciki kudade da kwangilolin Jami’ar Benue da ke Makurdi daga 2016 zuwa yanzu, duk hakan na cikin kokarinsa na dakile kofofin fata ne.
Har ila yau, gwamnan ya amince da aiwatar da sabon tsarin kammala aiki na shekaru 65 da tsawon lokaci na shekara 40 ga dukkanin malaman da suke jihar, bisa shawarwarin da TRCN ta bayar.
Za a iya cewa dai, kamun ludayin sabbin gwamnonin ya zama kadaran, kadahan musamman idan aka yi la’akari da tarin matsalolin da suka gada da kuma yadda cire tallafin mai ya haifar tun daga ranar da aka rantsar da su. Abin jira a gani dai shi ne, wane ne zai kai bantensa?
Katsina
A cikin kwana 100, abubuwan arzikin da Gwamnatin Jihar Katsina ta yi karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda, sun hada da tunkarar matsalar tsaro, inda ya amince da kashe kudade kimanin naira miliyan dubu 7.8.
Sannan Malam Radda, ya jagoranci samar da fili na wucin gadi wanda za a kafa Jami’an Kiwon Lafiya ta Gwamnatin Tarayya a Karamar Hukumar Funtua ta Jihar Katsina.
Bayan haka, Gwamnan ya ba da umarnin sayen shinkafa, inda za a kashe naira miliyan dubu biyu da Gwamnatin Tarayya ta baiwa jihohi.
Radda, ya ba da aikin fadada gadar Kofar Kaura da ta fara zama barazana, musamman ambaliyar ruwa; inda yanzu haka an kusa kammala ayyukan wannan gada.
Haka kuma, gwamnan ya ba da umarnin a fitar da miliyoyin nairori, domin daukar nauyin wadanda iftila’in ‘yan bindiga ya shafa a Jihar Katsina.
Abu na farko da Gwamnan Jihar Katsinan, Malam Dikko Umar Radda ya fara shi ne, cire masu rike da mukaman siyasa wadanda ya gada daga tsohon Gwamna Aminu Bello Masari.
Sai kuma, yadda Gwamna Raddan ya dakatar da manyan sakatarori daga mukamansu kafin daga baya ya kafa wani kwamiti da zai shirya jarrabawa ga duk wanda ke san zama Babban Sakatare.
Da yawa daga cikinsu, sun fadi wannan jarrabawa da aka ce an dauko wani kwararre daga Jihar Barno, domin shiryawa.
Haka kuma, gwamnan ya yi tafiye-tafiye har sau goma sha daya zuwa Abuja, sannan ya fita kasashen waje sau uku, inda yanzu haka ya bar kasar kusan kimanin kwana goma.
Har ila yau, Malam Dikko Radda ya ba da umarnin Kananan Hukumomin Jihar Katsina 34, su sayi masara domin raba wa jama’a, sai dai har gobe jama’a na tambayar nawa aka kashe wajen sayen wannan masara, batun da har gobe babu amsa daga bangaren gwamnatin
Bayan haka, Gwamnatin Radda ta dawo da dokar hana hawa babur a wasu garuruwa da ke fama da matsalar tsaro, batun da masana ke cewa, dokar ba ta haifar da da mai ido ba.
Kebbi
Tun daga ranar 29 ga mayun shekarar 2023, da Gwamna Nasir Idris ya karbi karagar madafun iko a Jihar kebbi, wanda zuwa wannan wata na Satumba, yana kasa da kwanaki 100 a kan karagar mulkin jihar. Amma duk da haka, gwamnan ya mayar da hankalinsa wajen tabbatar shinfida sababin hanyoyi a cikin kwaryar babban Birnin Jihar ta Kebbi.
Inda a ranar 25 ga watan Yuli, ya ba da kwangilar shinfida sabbin hanyoyin motoci na cikin babban Birnin Jihar guda biyar, a kan naira bilyan 9.4, ga Kamfanin Habib Engineering Nig. Limited, inda ake sa ran kammala aikin a cikin wata goma sha takwas masu zuwa. Aikin shinfida sabbin hanyoyin, zai soma ne tun daga hanyar shigowa jihar, wato NNPC Mega har zuwa shataletalen RIMA, har zuwa bakin Ofishin Hukumar NDLEA, ya kuma tashi zuwa shataletalen gidan man AP 2, wato hanyar fita daga garin Birnin na Kebbi.
Haka zalika, abubuwan da za a sanya a manyan titunan sun hada da, hasken wutar lantarki mai aiki da hasken rana (solar street lights), ga hanyoyin guda biyar da kuma shuke-shuke na zamani.
Haka nan kuma, gwamnan ya ba da umarnin biyan kudaden tallafin karatu ga daliban da ke karatu a Jami’o’in Kasar nan, ‘yan asalin Jihar Kebbi, wadanda aka tantance a jami’o’in daga shekarar 2023 zuwa 2024.
Kazalika, ya sanya hannu tare da amincewa da kashe kimanin naria milyan 92.2, domin sayo sinadaren kemikal; don inganta samar da ruwan sha ga al’ummar jihar baki-daya. Har wa yau, an sake fito da wani shiri na tallafi tare da inganta rayuwar kasuwancin masu karamin karfi da kuma marasa karfin baki-daya, wato KB-CARES; inda aka ba da tallafi ga mutane dubu ashirin a dukkanin fadin Kananan Hukumomi 21 na jihar, wanda mata da maza matasa suka samu cin gajiyarsa, inda aka baiwa marasa karfi naira dubu dari, sai kuma masu karamin jari naira dubu dari da hamsi kowannensu.
Shirin dai, an tsara shi ne domin tallafa wa mutane dubu ashirin da takwas, inda kashin farko na shirin kawo yanzu ya tallafa wa mutane dubu ashirin a Kananan Hukumomi 20. Kashi na biyu kuma zai tallafa wa mutane dubu takwas.
Har ila yau, Gwamnatin Gwamna Nasir Idris a ranar 19 ga watan Augusta 2023, ta ba da kwangilar kammala aikin Sakatariyar Ma’aikatar da ke a Gwadangaji, kan kudi naira biliyan 10 ga kamfani biyu, ana sa ran kammala aikin Sakatariyar a cikin wata goma sha takwas kacal, kamfanunuwan da aka baiwa aikin sun hada da, ‘MTECH Unibersal Concept Limited’ da kuma ‘ZBCC Limited’, haka kuma an kasa aikin gida biyu; wato Lot A da Lot B.
Aikin ginin Sakatariyar, tun a farkon Gwamnatin Tsohon Gwamna Saidu Usman Dakingari, aka ba da Kwangilar ga Kamfanin ‘Rockwell Nig. Limited’ a kan kudi naira biliyan 3.8, daga baya aka koma bitar kwangilar, saboda tashin kayan aiki zuwa naira biliyan 7.7, a watan Disamba na shekarar 2015. Bisa ga haka ne Gwamna Nasir Idris, ta kara ba da wannan kwangila domin kammala aikin.
Yanzu haka, Gwamnatin Jihar tana kan bayar da tallafin rage radadin janye tallafin man fetur ga al’ummar jihar. Bugu da kari, a watan da ya gabata, Gwamna Nasir Idris ya kaddamar da rabon taki ga al’ummar jihar kyauta, wanda manoma a jihar suke ta yaba masa tare da sanya albarka.