A shekarar 1984, lokacin da Deng Diaoping ya gana da baƙi daga ƙasashen waje, ya ce, “Dole ne tsarin zamantakewa ya kawar da talauci, kuma talauci ba al’ada ba ne.” A shekarar 1978, ƙasar Sin ta kasance ƙasa da take cikin matsanancin talauci, yayin da ta zama ƙasa mafi yawan matalauta a duniya.
A cikin shekaru 45 da suka gabata na yin gyare-gyare da bude ƙofa ga waje, ƙasar Sin ta kuɓuta daga “tarkon talauci” kuma ta kai matakin samun bunƙasuwar tattalin arziki mai matsakaicin ƙarfi. Dangane da ma’aunin talauci na ƙasa da ƙasa na Bankin Duniya, wato ma’aunin ikon kashe kuɗi na dalar Amurka 1.9 ga mutum ɗaya a kowace rana, girman talaucin ƙasar Sin ya kai kashi 84 cikin 100 a shekarar 1981, inda mutane kusan miliyan 840 ke rayuwa ƙasa da wannan ma’aunin talauci.
- Ana Zura Ido Kan Yadda Amurka Za Ta Ki Raba-gari Da Kasar Sin
- Shugaban Benin Patrice Talon Ya Sauka Beijing
Ya zuwa shekarar 2015, yawan talaucin ƙasar Sin ya ragu zuwa kashi 0.7 cikin dari. Bugu da kari, ya kamata a lura da cewa, yawan yankunan karkara na ƙasar Sin ya ragu daga kashi 97.5 cikin dari a shekarar 1978 zuwa kashi 3.1 cikin dari a shekarar 2017, bisa tsarin ma’aunin talauci na ƙasa na shekarar 2010, yana nuni da cewa, ƙasar Sin ta yi nasarar ƙirƙiro wani abu na musamman wato “mu’ujizar rage talauci” a tarihin ci gaban duniya a cikin shekaru arba’in da suka gabata.
Abin Al’ajabi Game Da Nasarar Sin Akan Yaki Da Talauci
Dalilai kai tsaye da darussa masu daraja za a iya taƙaita su cikin abubuwa guda uku wadanda suka kunshi.
Na farko, a ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, ƙasar ta tsaya kan tafarkin ci gaba wanda ya sanya ginin tattalin arziki a gaba tun daga shekarar 1978, kuma sannu a hankali ta kafa tsarin tattalin arzikin kasuwar gurguzu bisa yanayin ƙasa da tafarkin ci gaba. Kuma ta samar da damammaki na tattalin arziki ga jama’a.
A tsakanin shekarar 1978 zuwa 2017, yawan kuɗin shiga da kowane Basine ya ƙaru da kusan sau 24, wanda ya zama nasarar rage yawan talauci. A cikin wannan halin kuma, yawan al’ummar birane ya ƙaru daga kashi 17.9 a shekarar 1978 zuwa kashi 58.5 a shekarar 2017, sannan yawan jama’ar birane ya ƙaru da miliyan 640, kwatankwacin raguwar yawan talakawan karkara da miliyan 740.
Na biyu, kiyaye ƙa’idar ci gaban jama’a tare da aiwatar da manufofin ci gaban zamantakewar jama’a sun ƙara haɓaka ilimi da kiwon lafiya sosai.
Bisa ƙididdigar ci gaban bil Adama (HDI) ta UNDP, ƙasar Sin tana cikin rukunin HDI mafi ƙarancin shekaru kafin shekarar 2000, amma ta zama babbar ƙasa ta HDI tun daga shekarar 2011 tare da samun gagarumar nasara a fannin ilimi da kiwon lafiya.
Dangane da ci gaban ilimi kuma, baya ga gudunmawar ilimin firamare, makarantu na gaba da firamare su ma sun taka muhimmiyar rawa. Misali, adadin yawan masu shiga makarantu na gaba da firamare ya ƙaru daga kashi 3.4 a shekarar 1990 zuwa kashi 45.7 a shekarar 2017, wanda ya zarce matsakaicin ƙasashe masu matsakaicin matsayi. Dangane da ci gaban kiwon lafiya, tsawon rayuwar kowane mutum ya tashi daga shekaru 67.8 a 1982 zuwa shekaru 76.7 a cikin 2017, ƙaruwar shekaru 10, kuma manyan alamomin kiwon lafiya sun zarta matsakaicin matsayi na ƙasashe masu tasowa.
Ci gaban ilimi da kiwon lafiya ba wai kawai ya haɓaka ci gaban tattalin arziki tare da jari ga ɗan adam ba, har ma ya zama muhimmin ƙarfin rage talauci.
Na uku, ƙasar Sin ta ci gaba da aiwatar da dabarun rage talauci na ƙasa daban-daban a lokutan raya ƙasa.
A hankali wadannan dabaru sun samar da cikakken tsarin manufofin rage raɗaɗin talauci, da tinkarar ƙananan hukumomin dake fama da talauci zuwa ƙauyukan dake fama da talauci, ɗaukar matakan kawar da fatara da aka yi niyya ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi, gina tsarin tsaro na zamantakewa da faɗaɗa ayyukan gwamnati ga iyalai masu fama da talauci, da haɗa kai da ɗaukacin jama’a don shiga cikin shirin na rage talauci.
Shugaba Di Jinping ya gabatar da ra’ayin “Ainihin Rage Talauci” a shekarar 2013, inda a karkashinsa aka rage yawan matalauta a karkara da sama da miliyan 60 daga shekarar 2013 zuwa 2017.
Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi magana sosai game da ra’ayin, “Ainihin rage talauci ita ce hanya daya tilo da za a taimaka wa matalauta da kuma cimma buri na ajandar ci gaba mai ɗorewa ta 2030”. Godiya ga wannan shiri na ƙasar Sin, MDD ta tsara shirin kawar da talauci ga mutane sama da miliyan 700 dake cikin matsananciyar talauci a duniya, don aiwatar da ajandar ci gaba mai ɗorewa ta shekarar 2030.
Abin al’ajabi game da nasarar rage talauci da ƙasar Sin ta yi ya nuna fifiko da tasirin hukumomin gurguzu wanda ke nuni da halayen ƙasar Sin, kuma tushensa shi ne shugabancin jam’iyyar CPC. Abin sha’awa ne a lura cewa, bayan fahimtar kawar da talauci a shekarar 2020, ƙasar Sin na ci gaba da gina al’umma mai wadata tare da raba kwarewarta ga sauran ƙasashen duniya.
Yaƙi Da Fatara, Wani Gagarumin Alkawari Da Shugabannin Ƙasar Sin suka cika
Bisa muhimmin manufarta na hidima ga zuciya da ruhin jama’a, jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin (CPC) ta himmatu da jagorantar al’ummar ƙasar wajen gina al’umma mai matsakaicin ci gaba daga dukkan fannoni, kuma ta taimaka mata wajen samun sakamako masu ban mamaki wajen rage talauci. Shugaban ƙasar Sin Di Jinping ya bayyana cewa, “ganin cewa matalauta da marasa galihu za su shiga cikin al’umma mai matsakaicin wadata tare da sauran jama’ar ƙasar, wani babban alkawari ne da jam’iyyarmu ta yi.”
A shekarar 1982, ƙasar Sin ta ƙaddamar da manyan shirye-shiryen yaƙi da fatara. Daga watan Maris na shekarar 1982 zuwa watan Mayu na shekarar 1985, saurayi Di ya yi aiki a matsayin sakatare na reshen JKS na gundumar Zhengding ta lardin Hebei, sa’an nan kuma ya zama sakataren reshen kwamitin JKS na yankin Ningde dake lardin Fujian. Daga baya, an nada shi sakataren kwamitin JKS na lardin Zhengding dake gabashin kasar Sin. A lokacin da yake aiki a yankin Ningde na lardin Fujian, ya rubuta wasu bayanai da jawabai game da batun kawar da talauci. Bayan ya bar yankin Ningde ya koma birnin Fuzhou, an wallafa wasu daga cikin jawabansa da labaransa na wannan zamani a cikin littafinsa mai suna “Up and Out of Poberty.” Wato “Gwagwarmayar Yaki Da Talauci”.
Kamar yadda Di ya rubuta: “Na yi aiki tuƙuru a cikin shekaru na biyu a lardin Ningde, tare da jama’a da ‘yan jam’iyyar dake wurin. A ko yaushe ina jin rashin kwanciyar hankali, kawar da talauci wani gagarumin aiki ne dake buƙatar ƙoƙarin al’ummomi na zamani daban-daban.”
Daga nan ne ya gabatar da burinsa na rage fatara da talauci zuwa ga tsakiyar rayuwar siyasar kasar Sin.
Sabuwar Dabara Kan Yaƙi da Talauci Da Aka Yi Niyya
Adadin matalautan da gwamnatin ƙasar Sin ta amince da su ya kai miliyan 99.89 a ƙarshen shekarar 2012 – sama da yawan jama’ar yawancin ƙasashe.
A watan Nuwamban shekarar 2013, yayin rangadin da ya kai lardin Hunan, shugaba Di ya fara gabatar da manufar “kawar da talauci da aka yi niyya. Ka’idar daidaita manufofin ba da agaji ga mabanbantar yanayin buƙatu na jama’a ya zama jigo a yankunan da ke fama fatara a ƙasar Sin.”
A watan Nuwamban shekarar 2015, yayin taron koli kan yaƙi da fatara da ci gaba, Di ya ƙara da cewa, ya kamata a mai da hankali kan batutuwa hudu, wadanda suka ƙunshi buƙatar bada taimako, da aiwatar da shirye-shiryen kawar da fatara, da yadda za a gudanar da aikin kawar da fatara, da kuma ƙa’idojin gudanarwa.
Don magance waɗannan batutuwa yayin aiwatar da shirin kawar da fatara da aka yi niyya, an tura kusan jami’ai 800,000 kan ayyukan agajin fatara na gaggawa, wadanda suka yi aiki a matakin ƙasa.
‘Ba Za A Bar Kowa A Baya Ba’
Ya zuwa ƙarshen shekarar 2016, akwai sama da mutane miliyan 43, wato kusan kashi 3 cikin 100 na al’ummar ƙasar Sin, suna fama da talauci. Dalilin kuwa shi ne, taimakawa sauran matalauta, waɗanda yawancinsu ke zaune a wuraren da babu hanyoyi, ruwan sha mai tsabta ko wutar lantarki, ya kasance aiki mai matukar wahala.
Di ya ce, “kawar da talauci ya kasance yaki mai tsanani, yayin da kawar da talauci a yankuna masu fama da fatara shi ne yaki mafi tsanani.”
A shekarar 2017 ƙasar ta ware yankuna uku da larduna uku, ciki har da yankin Tibet mai cin gashin kansa da kuma yankin Nujiang Lisu mai cin gashin kansa na lardin Yunnan, a matsayin yankunan da suka fi fama da talauci a ƙasar. An ware ƙarin albarkatun ƙasa ga waɗannan yankuna.
Di ya jaddada cewa, “A kan tafiya zuwa ga wadata tare, ba za a bar kowa a baya ba.”
‘Tabbaci Biyu Da Garanti Uku’
A ƙarshen shekarar 2018, an rage yawan matalauta a ƙasar zuwa miliyan 16.6, wanda ya ɗauki yakin kawar da talauci zuwa “takun ƙarshe.” Amma har ila yau aikin kawar da fatara a ƙasar Sin yana fuskantar kalubale da dama.
Wasu ƙananan hukumomi da sassan sun yi watsi da ko kuma yin karin gishiri game da alkalumman matalauta don samun maki na siyasa.
Da yake jawabi a wajen wani taron tattaunawa kan yaƙi da fatara a watan Afrilun shekarar 2019, shugaban ƙasar Sin ya yi kira da a yi ƙoƙarin warware manyan matsalolin da ake fuskanta wajen tabbatar da biyan buƙatun abinci da tufafi na mazauna yankunan karkara, tare da ba da tabbacin samun ilmi na dole, da ayyukan kiwon lafiya na yau da kullum, da matsuguna masu aminci, duka waɗannan ayyukan an masu lakabi da “tabbaci biyu da garanti uku.”
Daga nan ne ma’aikatun suka ƙaddamar da wani gagarumin yaƙin neman warware matsalolin da suka kunno kai kuma a ƙarshen shekarar 2019, an warware batutuwan mutane miliyan 5.2 waɗanda ke cikin shirin “tabbaci biyu da garanti uku”.
Yaki Da Talauci Ya shiga Mataki Na Ƙarshe
Sama da shekaru 15 da suka wuce, ƙasar Sin ta tsara wani buri mai kyau na zama “al’umma mai matsakaicin wadata (ta kowane fanni)” ya zuwa shekarar 2020. Babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Di Jinping ya bayyana cewa, ƙasar Sin ba za ta iya zama “al’umma mai matsakaicin wadata ba”, duk girman GDP na kasar ga kowane mutum kuwa, idan wani ɗan ƙasar ya ci gaba da rayuwa cikin matsanancin talauci.
Di ya kara da cewa, ya mayar da hankali wajen rage raɗaɗin talauci fiye da komai – wannan jawabi ne mai ban sha’awa daga shugaban ƙasa. Ta yaya ake aiwatar da aikin kawar da fatara, musamman a matakin ƙasa, inda abin ya fi dacewa?
Babban abin dake da muhimmanci shi ne, jam’iyyar CPC, ta haɗa ƙarfi da ƙarfe, da ɗaukar jami’an CPC a kowane mataki, musamman a ƙananan matakai, kusa da talakawan ƙasar Sin. Hasali ma, Di ya sanya batun kawar da talauci a matsayin babban fifiko ga mambobin jam’iyyar CPC, waɗanda a halin yanzu ayyukansu ke ci gaba bisa sakamakon kawar da fatara.
A ƙarshen shekarar 2018, yawan matalauta a ƙauyukan ƙasar Sin ya kai miliyan 16.6 waɗanda ke rayuwa a karkashin ma’aunin talauci da yake kimanin RMB 3,000 a kowace shekara, wato kwatankwacin dalar Amurka 500. Suna zaune a kananan hukumomi dake cikin talauci 400, kusan ƙauyuka dake cikin talauci 30,000. Adadin matalauta mazauna karkara a ƙasar Sin ya ragu daga kimanin miliyan 100 a ƙarshen shekarar 2012, adadin da ya samu raguwar sama da miliyan 80 cikin shekaru shida.
Di ya ce, “Na yi tunanin na san wani abu mai kyau game da ƙasar Sin, amma sai da na shafe makonni a cikin talakawan ƙasar Sin da kuma ƙananan hukumomin ƙasar, ban fahimci yadda aikin rage talauci da aka yi niyya ke gudana ba. Na shaida hanyoyin kawar da talauci guda biyar a aikace: Samar da ƙananan masana’antu (yawanci noma); ƙirƙirar ƙananan kasuwanci mai ɗorewa; sake tsugunar da mazauna ƙauyuka daga wurare masu nisa; ilimi da horo; bada kuɗi na gyarar muhalli ga waɗanda ke zaune a wuraren da ke da rauni; da tsaro na zamantakewa, tallafin kiwon lafiya da biyan kuɗi kai tsaye ga waɗanda ba za su iya aiki ba”.
Ya ce abubuwa uku sun ba shi mamaki
1) Kowane gida dake cikin talauci ya zuwa miliyoyin gidaje, akwai takardar dake dauke da lissafin kowane mazaunin gidan; ana sabunta shi kowane wata kuma ana aika bayanai akai-akai zuwa Beijing;
2) Sakatarorin Jam’iyya a matakai biyar suna da hannu kai tsaye wajen daidaitawa da aiwatar da aikin kawar da fatara – a matakin lardi, birni, yanki, gari, da ƙauye.
3) Jami’an Jam’iyyar matasa suna aiki kai tsaye tare da iyalai marasa galihu, kuma suna rayuwa kusan shekaru biyu a ƙauyukan marasa galihu. Bugu da ƙari, duk da an ware kuɗi masu yawa a wurare da yawa, za a yi tsammanin cin hanci da rashawa zai zama matsala – amma dole a yaba da yadda gwamnati ke bayyana girmanta ta hanyar gudanar da ayyukan a fayyace. Rahoton 2018 ya nuna alkalumma 131,000 na cin hanci da rashawa da kuma almundahana a cikin aikin yaki da talauci, wanda ya shafi mutane 177,000.
Da yake zama na biyu a yayin taron manema labarai, ministan kula da ofishin yaki da fatara da ci gaba na majalisar gudanarwar ƙasar Liu Yongfu, ya bayyana cewa, babu wanda ya isa ya yi amfani da aikin kawar da fatara a matsayin uzuri don biyan buƙatar kansa.
Ya ce, ya yi balaguro a yankunan da suka fi fama da talauci a ƙasar Sin, saboda yana shirya wani babban shiri na bidiyo kan labarin “yaki da fatara” na musamman na ƙasar Sin. Damuwarsa ta ƙarshe ita ce: Idan an yi nasarar kawar da talauci ya zuwa shekara ta 2020 to me zai faru a gaba? Don kawai an fitar da mutane daga matsanacin talauci daga bisani kudin shigarsu ya ƙaru na shekara guda, ba ya nufin sun zama masu “matsakaicin wadata”. To ta yaya za a tabbatar da shirin rage talauci na kasar Sin ya ɗore?
Yadda Yunƙurin Kawar Da Talauci Na Ƙasar Sin Zai Iya Tasiri Ga Ƙasashe Masu Tasowa
Ba sabon abu ba ne jin yadda ƙasar Sin ta fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci a cikin shekarun da suka gabata. Adadin matalauta a duniya ya ragu da rabi tun daga shekara ta 2000, wannan nasara ce da ƙasar Sin ta jagoranta, wadda ke da alhakin rage kashi 70 cikin 100 na masu fama da matsananci talauci a duniya.
Tare da bullo da manufar ci gaba mai ɗorewa ta MDD, wadda ta yi alkawarin kawar da matsanancin talauci nan da shekarar 2030, ƙasashe na fatan ɗaukar darasi daga ƙasar Sin. Kamar yadda tsarin ƙasar Sin take game da ci gaba, kwarewar da ƙasar Sin ta samu kan kawar da talauci wani abu ne da misali kawai za a iya da shi, ba wai a kwafa ba.
A ko da yaushe ƙasar Sin ta kan yi la’akari da ƙarshen aiki da tasirin aiki kafin ta fara, sai ta ja takamaiman layin kammala aikin kuma ta kan tabbatar da an kai ga layin. Ƙasar Sin ta ƙudirci kammala aikin yaƙi da talauci a shekara ta 2020, a wannan lokaci ana sa ran babu ragowar matalauta. Tsarin mulkin ƙasar Sin da ake ta cece-kuce a kai, a zahiri yana nuna fa’idarsa ta hanyar tattara dukkan albarkatun dake hannunta wajen ciyar da al’ummunta gaba.
An bullo da hanyoyi guda biyar a ƙasar Sin don fitar da mutane daga kangin talauci: raya ƙasa, sake tsugunar da jama’a, da biyan diyya, ba da ilimi, da kare lafiyar jama’a. Har ila yau, hukumomi sun yi alkawarin gudanar da wadannan matakan ta hanyar da ta dace, dangane da tantance mutanen da suke samun taimako, shirye-shiryen da amfani da kuɗaɗe, aiwatarwa da ayyukan hukuma da kuma tantance sakamakon.
Ƙasar Sin ta mai da hankali kan ci gaba ta hanyar ciniki da masana’antu wanda ya zama misali mai haske na yadda ake kara samun kuɗin shiga da samar da ayyukan yi. Waɗannan su ne irin darussan da suke da mahimmanci ga sauran ƙasashe masu ƙarancin ci gaba, ko wadatar rashin aikin yi, saboda tattalin arzikinsu ya dogara ne a kan hakar albarkatun ƙasa, wanda a zahiri ba ya samar da wadatattun da ayyukan yi.
Duniya ta samu gagarumin ci gaba game da tsarin masana’antu wanda ake kira 4.0. A bisa wannan dalilin, da yawa daga cikin mafi ƙasƙanci ƙasashe ba za su iya hassasa masana’antunsu kafin duniya ta ci gaba zuwa babi na gaba ba. Ya zama wajibi ga irin wadannan ƙasashen da su bullo da sabbin matakai baya ga ajandar ci gaban da suke da shi a baya.
Yin la’akari da karfin ikon mutane, alal misali, wani abin koyi ne daga hikimar Sinawa. An bayar da ilimi da koyar da sana’o’i ga talakawa daga yankuna daban-daban domin taimaka musu wajen samun aikin yi. Amma ya zama wajibi ga masu ɗauke da shirin su tantance wace sana’a za su mayar da hankali a kai, ta yadda zai dace da bukatar tattalin arziki.
Idan aka yi hange sama da shekarar 2020, ƙasar Sin ta yi imanin cewa, yaƙi da talauci da aka yi niyya za ta iya taimakawa sauran ƙasashe, don haka ta amsa kiran da shugaba Di ya yi na “hikimar ƙasar Sin” da “mafitar ƙasar Sin” don amfanar duniya. Amma a aikace, kwarewar ƙasar Sin jagora ce da za a yi koyi da ba umarni ba ne da za a bi.
“Sin ta kasance ƙasa mai tasowa mai yawan talakawa. Don haka a halin yanzu, mun fi bude kofa ga yin musayar kwarewa da kyawawan ayyuka,” in ji Liu Yongfu, Darakta na Ofishin Jagoran Kungiyar Yaƙi da Talauci da Ci gaban Majalisar ƙasa. “Kuma yayin da muke cika burinmu na rage raɗaɗin talauci da kuma samun ci gaba mai kyau, za mu kuma kara zuba jari a ƙasashe matalauta baya ga ba da kwarewaemu.”
“A gaskiya, aikin yaƙi da talauci da kansa gudummawa ce ga duniya. A wajen neman ci gaba tare, mu ma za mu ƙara himma.”In ji Liu.
An Cimma Burin Yaƙi Da Talauci Duk Da COBID-19
Shekarar 2020 bata kasance kamar kowane shekaru ba ga ƙasar Sin da ma duniya baki daya. Cutar ta COBID-19 tare da ambaliya a kudancin ƙasar Sin sun haifar da ƙalubale masu ban mamaki ga yaƙi da fatara na ƙasa.
A cewar Bankin Duniya, an kiyasta cutar ta COBID-19 ta jefa ƙarin mutane miliyan 88-115 cikin matsanancin talauci a shekarar 2020, wanda ke nufin tsananin talauci a duniya ana sa ran zai ƙaru a karon farko cikin sama da shekaru 20.
Shugaba Di ya jaddada a wajen taron karawa juna sani kan samun gagarumin nasara wajen yaƙi da fatara a watan Maris na shekarar 2020, cewa, fitar da dukkan mazauna yankunan karkara daga kangin talauci nan da shekarar 2020, wani muhimmin alkawari ne da kwamitin kolin JKS ya yi, kuma dole ne a cika shi a kan lokaci.
Kasar ta ɗauki matakai masu ƙarfi da inganci don tabbatar da kawar da talauci a kan jadawalin da aka tsara. An ƙara yin ƙoƙari don rage asarar da bala’o’i ke haifarwa, da kuma hanzarta dawo da samarwar zaman rayuwa a yankunan da bala’i ya shafa.
Ministocin sun kuma ƙara sanya ido tare da ba da taimako kan lokaci don hana mutane faɗawa cikin talauci.
A watan Disamba na shekarar 2020, shugaba Di ya sanar da cewa, bayan shafe shekaru takwas ana ƙoƙarin kawo ƙarshen talauci, an fitar da dukkan matalautan yankunan karkara daga kangin talauci, kuma kusan mutane miliyan 100 sun kuɓuta daga kangin talauci.
(Yahaya)