Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanata a Kano ta tsakiya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa zaiyi kokarin ganin matasa sun cika burikansu idan ya zama shugaban kasa a shekarar 2023.
Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a jihar Gombe, a ranar Asabar, a yayin bude ofishin jam’iyyar NNPP na jihar.
Tsohon gwamnan, wanda Kuma tsohon ministan tsaro ne shine dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar NNPP a babban zabe mai zuwa.
Ya ce, dadewar da yayi a fagen siyasa da kuma irin mukaman da ya rike a baya sune suka taimaka wajen kafuwar jam’iyyar NNPP a fadin kasar nan a cikin lokaci kadan.
Ya ci gaba da cewa idan har jam’iyyar bata fitar da dan takarar Shugaban kasa ba a wannan lokacin tabbas zata mutu.
Kwankwaso ya tabbatar da cewa har yanzu suna tattauna wa da Peter Obi, dan takarar Shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar LP, domin hadewa waje daya sai dai yace babbar matsalar da suke fuskanta a tattaunawar shine wanda zai zama dan takarar Shugaban kasa.
“Wasu daga cikin wakilan mu a yayin tattaunawar sun bukaci dole a duba cancanta da kwarewa da shekaru da takardar shaidar karatu idan ana son zabar wanda zai zama dan takarar Shugaban kasa idan za’a hade” in ji Kwankwaso.
Ya Kara da cewa “Idan har na amince zan zama Mataimakin shugaban kasa tabbas NNPP zata mutu saboda jam’iyyar tana tafiya ne akan aikin da mukayi na tsawon shekara 30 a rayuwar mu”
Kwankwaso ya ce, “Nayi shekara 17 Ina aikin gwamanti ga shekara 30 Kuma ina siyasa, shekara 47 kenan”
Ya ci gaba da cewa abu mafi sauki ga al’ummar kudu maso arewa shine suzo a hadu a NNPP domin idan ba’a hade ba Kuma basu samu shugaban cin kasar nan ba sunyi mummunar asara.