• Leadership Hausa
Saturday, December 9, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matasa Za Su Yi Rayuwa Mai Kyau Idan Na Zama Shugaban Kasa —Kwankwaso

by Sulaiman and Abba Ibrahim Wada
1 year ago
in Labarai
0
Matasa Za Su Yi Rayuwa Mai Kyau Idan Na Zama Shugaban Kasa —Kwankwaso
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanata a Kano ta tsakiya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa zaiyi kokarin ganin matasa sun cika burikansu idan ya zama shugaban kasa a shekarar 2023.

Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a jihar Gombe, a ranar Asabar, a yayin bude ofishin jam’iyyar NNPP na jihar.

  • Sanatocin APC 3 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP da NNPP

Tsohon gwamnan, wanda Kuma tsohon ministan tsaro ne shine dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar NNPP a babban zabe mai zuwa.

Ya ce, dadewar da yayi a fagen siyasa da kuma irin mukaman da ya rike a baya sune suka taimaka wajen kafuwar jam’iyyar NNPP a fadin kasar nan a cikin lokaci kadan.

Ya ci gaba da cewa idan har jam’iyyar bata fitar da dan takarar Shugaban kasa ba a wannan lokacin tabbas zata mutu.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Katsina Ta Kara Jaddada Matsayinta Kan Bunkasa Ilimi

An Bukaci Gwamnatin Kaduna  Ta Samar Da Hukumar Zakka Da Wakafi

Kwankwaso ya tabbatar da cewa har yanzu suna tattauna wa da Peter Obi, dan takarar Shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar LP, domin hadewa waje daya sai dai yace babbar matsalar da suke fuskanta a tattaunawar shine wanda zai zama dan takarar Shugaban kasa.

“Wasu daga cikin wakilan mu a yayin tattaunawar sun bukaci dole a duba cancanta da kwarewa da shekaru da takardar shaidar karatu idan ana son zabar wanda zai zama dan takarar Shugaban kasa idan za’a hade” in ji Kwankwaso.

Ya Kara da cewa “Idan har na amince zan zama Mataimakin shugaban kasa tabbas NNPP zata mutu saboda jam’iyyar tana tafiya ne akan aikin da mukayi na tsawon shekara 30 a rayuwar mu”

Kwankwaso ya ce, “Nayi shekara 17 Ina aikin gwamanti ga shekara 30 Kuma ina siyasa, shekara 47 kenan”

Ya ci gaba da cewa abu mafi sauki ga al’ummar kudu maso arewa shine suzo a hadu a NNPP domin idan ba’a hade ba Kuma basu samu shugaban cin kasar nan ba sunyi mummunar asara.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Mun Shirya Tsaf Don Gudanar Da Zaben Gwamna A Jihar Osun —INEC

Next Post

Hukumar Kashe Gobara A Jihar Kano Ta Ceto Mutum 135 A Watan Yuni

Related

Gwamnatin Katsina
Labarai

Gwamnatin Katsina Ta Kara Jaddada Matsayinta Kan Bunkasa Ilimi

11 hours ago
Zakka
Labarai

An Bukaci Gwamnatin Kaduna  Ta Samar Da Hukumar Zakka Da Wakafi

12 hours ago
Hatsarin Jiragen Ruwa
Labarai

Hatsarin Jiragen Ruwa: Sakacin Hukumar Kula Da Hanyoyin Ruwa Ya Janyo Mutuwar Mutum 911

13 hours ago
Tashin Bom
Manyan Labarai

Tashin Bom A Kaduna: Yadda Na Tsallake Rijiya Da Baya – Dattijo Mai Shekara 74

14 hours ago
Game Da Tambayar Nan:  Ko Ka Yi Tir Da Harin Ranar 7 Ga Oktoba?
Labarai

Game Da Tambayar Nan: Ko Ka Yi Tir Da Harin Ranar 7 Ga Oktoba?

21 hours ago
Rawar Da Nijeriya Ta Taka A Taron Dumamar Yanayi Na Duniya
Labarai

Rawar Da Nijeriya Ta Taka A Taron Dumamar Yanayi Na Duniya

23 hours ago
Next Post
Gwamnatin Kano Ta Dauki Karin Masu Share Tituna Don Tsaftace Muhalli

Hukumar Kashe Gobara A Jihar Kano Ta Ceto Mutum 135 A Watan Yuni

LABARAI MASU NASABA

COP28: Sin Da Afirka Za Su Bunkasa Hadin Gwiwa A Fannin Raya Kananan Ayyukan Samar Da Makamashi Mai Tsafta

COP28: Sin Da Afirka Za Su Bunkasa Hadin Gwiwa A Fannin Raya Kananan Ayyukan Samar Da Makamashi Mai Tsafta

December 9, 2023
NOMA

Kurakuran Da Wasu Ke Tafkawa A Noma Don Kasuwanci

December 9, 2023
Ministan Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Mali

Ministan Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Mali

December 9, 2023
IFAD

Manoman Karkara Sun Nuna Farin Ciki Da Yadda Suka Amfana Da Tallafin IFAD

December 9, 2023
NPA

NPA Ta Bayyana Dalilan Dawo Da Kwangilar Kamfanin INTELS

December 9, 2023
Nijeriya

Kayan Da Nijeriya Ke Fitarwa Waje Sun Karu Zuwa Naira Tiriliyan 10.35

December 9, 2023
harkokin zabe

Amfani Da Fahasa Zai Bunkasa Harkokin Zabe –Agu

December 9, 2023
TGI

TGI Group Za Ta Hada Kai Da ABU Domin Bunkasa Kirkire-kirkire

December 9, 2023
Tinubu

Tinubu Zai Sake Fuskantar Wata Shari’ar A Kotun Koli Kan Zaben 2023

December 9, 2023
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Za Ta Zaftare Kudaden Kananan Hukumomin Da Ba A Yi Zabe Ba

December 9, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.