A cikin wannan makon ne, gwamnatin Jihar Kano ta bayyana rage kudin makarantun gaba da sakandare da kasho 50.
Kwishinan ilimi mai zurfi na Jihar Kano, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata ne ya bayyana hakan, inda ya ce Gwamnatin Kano ta yi la’akari da matsanancin halin matsin tattalin arziki da al’ummar ke fuskanta a halin yanzu, wanda hakan ta sa gwamnati ta zabge kaso 50 na kudin karatu ga dalibai ‘yan asalin Jihar Kano da ke karatu a makarantu gaba sakandire mallakar Jihar Kano.
- Abubuwa Takwas Da Gwamnatin Tinubu Za Ta Bai Wa Fifiko
- Dan Daba Ya Yi Wa Dan Jarida Dukan Tsiya A Cikin Gidan Gwamnatin Adamawa
Ya ce gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, gwamna ne mai kyakkyawan fatan ga al’ummar Jihar Kano ya bayar da wannan tabbaci ranar Talatar da ta gabata.
Gwamnan Abba ya bayar da umarnin a gaggawa yanke kaso 50 na kudaden da daliban Kano ke biya a makarantun gaba da sakandire domin rage radadin tattalin arzikin da al’umma ke fama da shi a ‘yan kwanakin nan a fadin kasa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp