Gwamatin Katsina ta sanya dokar ababen hawa a wasu kananan hukumomin jihar.
Gwamnatin Katsina ta jaddada cewa dokar nan ta dakile tsaro wadda gwamna ya sanya wa hannu tun ranar 31 ga watan Yulin wannan shekara har yanzu tana aiki.
- Da Goyon Bayanku Zamu Lashe Firimiyar Nijeriya —Kyaftin Din Katsina United
- Kyakkyawar Alakar Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Na Haifar Da Ci Gaba Mai Armashi
Sanarwar hakan ta fito ne daga ofishin kwashinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa.
Sanarwar ta ce tun lokacin da dokar ta fara aiki, dukkanin motocin da ke dauko itace da shanu daga dazuka an haramta ayyukansu, sannan kuma an dakatar da saida shanu a kasuwannin Safana, Danmusa, Batsari, faskari da kuma Sabuwa kwata-kwata.
Sanarwar ta kara da cewa dole ne kuma sai an samu tantancewa “clearance” daga hakimi, magaji ko dagaci a kan daukar shanu daga Jihar Katsina zuwa duk wata jiha a Nijeriya.
Sai dai kuma a karanan hukumomin Dandume, Funtua, Faskari, Bakori, Matazu, Kankara, Danja, Kafur, Malumfashi, Musawa, Matazu, Danmusa, Safana, Dutsinma, Kurfi, Charanchi, Jibiya, Batsari da kuma Kankiya, dor harmcin hawan baburan hayar tana farawa ne daga karfe takwas na dare zuwa karfe shidda na safe.
Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida ya ce gwamna Malam Dikko Umar Radda ya sanya wa dokar hannu ne da nufin dakile matsalar tsaro da ake fama da ita.