An kama wani mutum mai suna Adejumo, da ake zargi da yin sojan gona na jami’in Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa Ta Jihar Legas, da laifin janyo mota a Legas.
PUNCH Metro ta gano a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa wanda ake zargin ya tuko wata mota mai fentin LASTMA a jikinta kuma ana zarginsa da sato motar gami da janyo ta da sanyin safiya a unguwar Somolu da ke Legas.
- Sarkin Musulmi Ga Malamai: Ku Rika Shawartar Masu Mulki Kan Shugabanci Nagari
- Xi Ya Taya Wata Jami’a Murnar Cika Shekaru 70 Da Kafuwa, Sannan Zai Ba Da Jawabi A Yayin Bikin Bude CIFTIS Na 2023
A cikin faifan bidiyon, an ji wata mata da har yanzu ba a bayyana sunanta ba, mai yiwuwa ita ce mamallakiyar motar kirar Acura MDD, tana ihun cewa an sace motar ta ne ta hanyar amfani da motar jawo motoci ta LASTMA.
Ta ce, sandar da aka makala a jikin motar domin janyo ta ce ta karye, sannan direban motar ya fita ya gudu bayan da mazauna garin suka yi masa ihun barawo.
“Ban taba tsammanin cewa za a yi amfani da motar janyo motoci a sace mota ba. Alhamdu lillah, kawai sai jama’ armu suka tashi suka fara ihu, yayin da mutane suka yi ta ihu sai barayin suka ruga da gudu suka bar komai nasu a wurin,” in ji matar.
An ga motar da aka janyo ta kakare a bayan sandar da aka makala sarkar janyo motar ya ta karye.
Da yake bayani a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, Daraktan hulda da wayar da kan jama’a na LASTMA, Adebayo Taofik, ya ce an kama direban motar.
Adebayo ya ce, “Direban motar da ya tuko motar janyo motocin ba jami’in LASTMA ba ne. Yana da kyau a sanar da jama’a, musamman masu ababen hawa cewa an kama direban, Adejumo, kuma a yanzu haka yana ofishin ‘yansanda na Pedro domin ci gaba da bincike.”
Ya kara da cewa bincike ya nuna cewa “Direban motar da aka kama ya yi kama da daya daga cikin masu safarar motocin LASTMA da katin shaida na bogi da tambarin LASTMA na jabu.”
Ya kara da cewa Babban Manajan Hukumar LASTMA, Mista Bolaji Oreagba, ya roki jama’a da su yi hattara da miyagu masu kokarin bata sunan hukumar.