• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Harin ‘Yan Bindiga A Kauyen Dan-Umaru: ‘Yansanda Sun Kwato Roka A Kebbi

by Umar Faruk
2 years ago
in Labarai
0
An Kama Masu Fataucin Kananan Yara A Ribas
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi, ta kwato  wani makamin roka guda daya da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi watsi da su a kauyen Dan-Umaru da ke gundumar Bena a Karamar Hukumar Danko-Wasagu ta jihar.

Bayan samun wannan bayanin ne tawagar ‘yansanda daga sashen ‘yansanda na Dan-Umaru, suka ma-yar da martani cikin gaggawa da ruwan harsashi.

  • Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Wani Limami A Abuja Da Sanata Ndume 6 Ga Satumba
  • An Kaddamar Da Shirin Baje Kolin Inganta Harkar Noma Da Sana’o’i A Kano

Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Samuel Titus Musa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Birnin Kebbi, yayin da yake gabatar da wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a shalkwatar rundu-nar jihar.

Kwamishinan ya ce “Tawagar ‘yansandan sun yi nasarar dakile harin tare da gano makamin roka guda daya, da ‘yan bindigar da ake zargin sun tsere da raunukan harbin bindiga daban-daban.

Haka kuma ya kara da cewa, wani Aminu Bello dake Unguwar Almasira a cikin garin Jega, ya karbo bash-in Naira 485,000 daga abokinsa Abdulmajid Nasiru. Wanda ake zargin, Aminu Bello ya yaudari wanda abin ya shafa ya ja shi zuwa cikin wani daji da ke kusa da su inda ya daba masa wuka a wuya.

Sakamakon haka, wanda aka daba wa wukar ya fadi a sume kuma aka garzaya da shi babban asibitin Aisha Muhammadu Buhari da ke Jega inda wani likita da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa. Daga nan sai jami’an ‘yansanda suka kama wanda ake zargin wanda ke shirin tserewa.

A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa. A cewar kwamishinan ‘yansanda, bayan an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Hakazalika, an kama wata mata Mai suna Hauwa Sulieman dake kauyen Babbar Dogo dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, tana rike da harsashi harsashi guda dari biyar da sittin da shida (566) 7. 62×39mm. Ana gudanar da bincike kan lamarin. Da yake jaddada cewa an kama ta ne a yankin na kara-mar hukumar Danko-Wasagu a ranar 24 ga Yuli, 2023.

A wata hira da ta yi ‘yar jarida a shalkwatar ‘yansanda da ke Birnin Kebbi, ta ce “Wata mata ce ta nemi in taimaka mata na karbo musu sako a madadinta, daga nan na bube jakar da na ga harsashi, na isa wajen jami’an tsaron soji da ke bakin aiki a Karamar Hukumar Danko-Wasagu, sai na sauka kan mota inda na same su daga nan na yi musu bayani kuma na mika musu harsashi, in ji ta”.

A cewarta, bai dace in bari a yi amfani da wannan harsashi wajen kashe dan’Adam ba, domin a matsay-ina na Musulma ta gari me zan fada wa Allah Madaukakin Sarki ranar haduwata da shi. “Ban da wani  zabi ban da in bayar da rahoto game da harsashin,” in ji ta.

“Bayan sun yi min tambayoyi su jami’an soji suka yi mani, sun kama ni, daga baya suka mika ni ga ‘yan-sanda, a cewar Hauwa Sulieman.” Sai dai ta ce, “Na san cewa mallakar harsashi laifi ne, shi ya sa na kai rahoto ga jami’an soji da ke bakin aiki a wurin da na ambata a sama,” in ji ta.

Kwamishinan, ya bayyana jin dadinsa ga mukaddashin Sufeto Janar na ‘yansanda Kayode Adeolu Egbe-tokun da ya ga ya dace da a turo shi Jihar kebbi a matsayin Kwamishinan ‘yansanda na 35.

A yayin da yake tabbatar wa IGP da gwamnatin Jihar kebbi da daukacin al’ummar jihar cewa jami’an rundunar da ke karkashinsa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin Jihar Kebbi da kewaye ta samu ‘yanci daga duk wani nau’i na aikata laifuka.

Bisa ga hakan ya yi kira ga jama’a a fadin jihar da su taimaka wa ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro wajen ba da muhimman bayanai na duk wani motsi ko aiki da ake zargin laifi ne. Domin ta hanyar bayar da bayanai ne za mu iya yin aikin namu kamar yadda doka ta tana da na dakile duk wani laifi, in ji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamna RaÉ—É—a Ya Raba Naira Miliyan 20 Ga Iyalan ‘Yan Sintirin Da Suka Rasu A Yaki Da ‘Yan Bindiga

Next Post

Dalilin Da Ya Sa Muka Dauki Matasa 7,000 Aikin ‘Yanbanga – Gwamnatin Kaduna

Related

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC
Labarai

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

3 hours ago
Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi
Labarai

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

3 hours ago
Daurarru
Labarai

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

13 hours ago
Wutar lantarki
Labarai

Fadar Shugaban Kasa Na Yunkurin Biyan Basukan Wutar Lantarki Na Naira Tiriliyan 2

15 hours ago
Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka
Labarai

Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka

16 hours ago
Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Kasuwar Waya A Kano
Manyan Labarai

Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Kasuwar Waya A Kano

16 hours ago
Next Post
Gwamnatin Kaduna

Dalilin Da Ya Sa Muka Dauki Matasa 7,000 Aikin ‘Yanbanga – Gwamnatin Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Neja

Dalilin Rashin Fara Aikin Kamfanin Takin Zamani Na Gwamnatin Jihar Neja

June 7, 2025
Adawa

Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027

June 7, 2025
2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

June 7, 2025
Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

June 7, 2025
Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

June 6, 2025
Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

June 6, 2025
Daurarru

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

June 6, 2025
Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata

Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata

June 6, 2025
Wutar lantarki

Fadar Shugaban Kasa Na Yunkurin Biyan Basukan Wutar Lantarki Na Naira Tiriliyan 2

June 6, 2025
Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka

Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka

June 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.