Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa daku acikin shirin namu mai farin jini da albarka na girki adon mata.
Abubuwan da ya kamata Uwargida ta tanada:
Shinkafa ta tuwo, gwargwadon yawan tuwon da zaki yi, Leda
Da farko zaki dora ruwanki a wuta
Sai ki wanke shinkafarki ki tsaneta so sai kidan baza tasha iska kinga wannan bazaki jika shinkafar ba idan ma kika wanke ta zaki tsane ta saboda ba’aso tasha ruwa, Idan ruwan ya tafasa sai ki kawo shinkafar ki zuba ki dan motsa da muciya kinga wannan ana dan motsawa ita kuma wadda zaki jika ba’a motsa kawai zubawa zaki yi kibarta tacigaba dahuwa sai ki rufe kibarshi ya dahu kamar dai yadda kika saba
Idan ya yi sai ki saukeshi ki tukeshi ki kwashe idan a leda kike sawa idan kuma malmalawa kike yi duk de yadda kike so.
 Miyar Hanta:
Abubuwa da uwargida zaki bukata
Hanta, Attaruhu,Tattasai, Albasa, Magi, Gishiri, Citta, Tafarnuwa, Kori, Onga, Mai.
Yadda ake hadawa
Da farko dai uwargida zaki wanke hantar kiyanka daidai misali
Sai ki sa a tukunya ki yanka albasa, kuma ki sanya magi kwaya daya da dan gishiri kadan haka
Idan yayi sai ki sauke ki kwashe a wani kwano, sai ki zuba mai da kayan miyanki wanda dama kin gyara su kin jajjaga ki soya ya soyu da kyau
Idan ya soyu sai ki zuba ruwa kadan ki sa hantar ki kawo magi, da gishiri, da citta da tafarnuwa wadanda dama kin dakasu ki zuba sannan ki zuba kori sai ki barshi ya yi kamar minti shabiyar zaki ji gida yadau kamshi sai ki sauke tadahu kenan. Aci dadi lafiya.