Mutum hudu daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka harbe a cikin masallaci a Kaduna sun bar iyalai da zawarawa 61 kamar yadda jaridar Daily Trust ta nakalto.
Idan za ku tuna dai wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun farmaki masallata a masallacin Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara a jihar Kaduna tare da kashe mutum bakwai a daren ranar Juma’ar da ta gabata.
‘Yan bindigar sun kai farmakin ne a kan Babura inda suka farmaki mutane da ke sallah acikin Masallacin, hakan ya basu damar kashewa da jikkata wasu da ke ibadar sannan daga bisani suka arce.
Wani tsohon manomi kuma dan kasuwa, Ya’u Ibrahim, wanda ke da ‘ya’ya 20 da mata biyu na daga cikin wadanda ‘yan bindigan suka kashe a wannan harin.
Sauran sun hada da kwamandan ‘yan banga na JTF wanda ake kyautata tsammanin shi ‘yan bindigar ke farauta, Malam Isiaka, wanda ya rasu yana da ‘ya’ya 17 da mata uku.
Kazalika, wani mazaunin kauyen, Yunusa Nuhu, an kasheshi ya bar ‘ya’ya 14 da mata biyu, yayin da kuma Malam Adamu na Gidan Maidara ya bar ‘ya’ya 10.
Malam Dan Asabe Saya-saya, sarkin kauyen, ya nuna harin a matsayin abun takaici da damuwa matuka.
Ya bayyana cewar wani Mustapha Sale, dan shekara 25 a duniya, shi ne kawai daga cikin wadanda aka kashe din bai da mata.
“Kamar yadda kuka sani, mutum biyar a cikin masallacin kauyen aka kashe su, yayin da aka kashe wasu hudu kuma a kauyukan da ke makwafta. sannan, hudu daga cikin wanda aka kashe sun bar duniya da ‘ya’ya da mata 61,” ya shaida.
“Mutum daya ne kawai bai da aure, kuma shi ma an riga an gama shirye-shiryen aurensa wannan harin ya rutsa da shi.”
Ya ce, iyalan mamatan suna tsananin bukatar tallafi da taimako a halin yanzu domin yadda za su iya rike kansu da ‘ya’yansu.