• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Zamfara Ta Bada Umurnin Ɗaukar ‘Yan Sa-kai

Za Ta Gina Tare Da Sabunta Azuzuwa Sama Da 200

by Leadership Hausa
2 years ago
Zamfara

A jiya Litinin ne gwamna Dauda Lawal ya bayar da umurnin ɗaukar ‘yan sa-kai a matsayin ƙari ga ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi don magance matsalar tsaro.

Ɗaukar ‘yan sa-kai na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da aka tattauna a zaman majalisar zartaswar jihar Zamfara, wanda Gwamna Lawal ɗin ya jagoranta.

  • Gwamnatin Zamfara Ta Rufe Wasu Kasuwannin Shanu A Jihar

Wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce an gudanar da wannan zama na majalisar zartaswar ne a fadar gwamnatin jihar dake Gusau.

Ya ƙara da cewa, har wayau, a wurin taron majalisar ta bada umurnin a gina sabbin azuzuwan karatu, tare da sabunta wasu a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Jihar.

Ya ce: “A yunƙurinsa na ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaro, Gwamna Dauda Lawal ya aminta da ɗaukar ‘yan sa-kai a dukkanin ƙananan hukumomin Zamfara.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

“Duk dai a zaman majalisar zartaswar da ya jagoranta, ya aminta da ginawa, tare da sabunta azuzuwan karatu a faɗin ƙananan hukumomin.

“Za a ɗauki ‘yan sa-kai 300 a kowacce ƙaramar hukuma ta jihar. Waɗanda za a basu horaswar da ta dace, domin su ci gaba da taimakawa soji da ‘yan sanda kan yaƙi da ‘yan ta’adda.

“Majalisar ta aminta da gina sabbi tare da sabunta azuzuwan karatu guda 49 a Gusau, 11 a Anka, 15 a Bakura, 8 a Bukkuyum, 14 a Birnin Magaji, 8 a Bungudu, 8 a Gummi, 19 a Kauran Namoda, 8 a Maru, 11 a Maradun, 42 a Shinkafi, 8 a Talata Mafara, 27 a Tsafe da kuma guda 11 a Zurmi.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro
Labarai

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

October 20, 2025
Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta
Labarai

Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

October 20, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa
Ra'ayi Riga

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 20, 2025
Next Post
Kamfanin Makamashi Na Sin Ya Cimma Gagarumar Nasara A Fannin Karfin Wutar Lantarki Da Ake Iya Sabuntawa

Kamfanin Makamashi Na Sin Ya Cimma Gagarumar Nasara A Fannin Karfin Wutar Lantarki Da Ake Iya Sabuntawa

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025
Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

October 20, 2025
Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

October 20, 2025
Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

October 20, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 20, 2025
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a

October 20, 2025
Hukumar EFCC Ta Tsare Wasu Jami’anta 10 Bisa Zargin Karkatar Da Kayan Aiki

EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima

October 20, 2025
Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

October 20, 2025
Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

October 20, 2025
Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.