Kamfanin zuba jari a fannin makamashi na kasar Sin (China Energy), dake zama babban kamfanin samar da wutar lantarki bisa karfin kwal, ya sanar da samun gagarumar nasara wajen samar da makamashi mai tsafta da ake iya sabuntawa.
A cewar kamfanin, ya zuwa karshen watan Agusta, jimillar karfin makamashin da Sin ta yi amfani da shi, ya kai kilowatt miliyan 100.14, wanda ya kai wani gagarumin ci gaba a kokarin da take yi na sauyawa zuwa ga hanyoyin samar da makamashi mai tsafta.
Kamfanin ya ce, jimillar karfin wutar lantarkin da katafaren kamfanin ya samar, ya kai kilowatt miliyan 303.49, matakin da ba a taba ganin irinsa ba.
Alkaluma daga kamfanin sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Agusta, yawan jimillar karfin makamashi mai tsafta da wanda ake iya sabuntawa da kasar Sin ta shigar, ya karu daga kashi 25.8 bisa 100 a shekarar 2020 zuwa kashi 33 cikin 100, baya ga matsakaicin karuwar kashi 2.7 cikin 100 a shekara. (Ibrahim Yaya)