Bisa alkalumai masu dumi-dumi da kungiyar hada-hadar kudin kasar Sin ta fitar a yau Talata, an ce, kasuwar hada-hadar kudin kasar ta ci gaba da karuwa a watan Agusta.
Alkaluman sun nuna cewa, yawan cinikayyar hada-hadar kudin kasar a watan Agusta ya kai lots miliyan 949, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan triliyan 60.67, wato ya karu da kaso 47.76% bisa makamancin lokaci na bara.
Masanan da abin ya shafa sun bayyana cewa, bisa karuwar yawan alkaluman sayar da kayayyaki na kamfanonin kasar ko PMI na masana’antun kere-kere a watan Agusta, cinikayyar hada-hadar kudin kasar Sin ta kara habaka.
Ban da wannan, an lura cewa, daga watan Janairu zuwa watan Agusta na bana, gaba daya yawan cinikayyar hada-hadar kudin Sin ya kai lots biliyan 5.722, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan triliyan 373.81, adadin da ya karu da kaso 30.8% dari bisa makamancin lokaci na bara. (Safiyah Ma)