Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin a ranar Talatan nan ta sake nanata cewa, Taiwan ba ta da tushe, ko dalili ko hakkin shiga Majalisar Dinkin Duniya ko wasu kungiyoyin kasa da kasa da ke bukatar kasa ta zama mai ‘yanci kafin ta shiga.
An ba da rahoton cewa, mahukuntan Taiwan sun gabatar da jerin “bukatu hudu” game da shigar Taiwan MDD tare da yin ikirarin cewa za su gayyaci “abokan diflomasiyya” don mika wa babban sakataren MDD wasikar tare, da ke neman ya gyara kuskuren da MDD ta yi wa kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD, a cewar wani taron manema labarai na baya-bayan nan.
Da take mayar da martani, kakakin Mao Ning ta shaidawa taron manema labarai da aka saba yi cewa, bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan na kasar Sin daya ne. Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. Ko da yake bangarorin biyu sun dade suna adawa da juna a siyasance, amma ba a taba raba ikon mallakar kasa da cikakken yankin kasar Sin ba. Wannan shine ainihin yanayin batun Taiwan. Hasashen da hukumomin DPP suka yi na shigar Taiwan cikin tsarin MDD a hakika wani yunkuri ne na haifar da ra’ayi na karya game da kasar Sin a matsayin “kasar Sin kasashe biyu” ko “kasar Sin daya kuma Taiwan daya” da kuma kalubalantar tsarin kasa da kasa . (Yahaya)