An shawarci masu bukatar dauka ‘yar aiki, yar wanke-wanke da sauran masu yin hidmomi a cikin gidaje da su rika yin kwakkwaran bincike. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Legas Idowu Owohunwa ne ya yi wannan gargadin, bayan gabatar da wasu masu laifuka da aka kama a Legas kwanan nan.
An ruwaito labarain wani cewa, wani mutum da yake wanke-wake a wani gida ya kashe matar da yake aiki a gidanta ya kuma kashe mahaifiyarta, sannan kuma ya yi musu satay a kuma nemi ya arce. Dan wanke-wanken mai suna Joseph Ogbu, an yanke masa hukuncin kisa tun watan Maris bayan ya kashe uwargidansa mai suna Orewoluwa John mai shekaru 38 a duniya, da mahaifiyarta mai suna Adejoke mai shaekaru 89 a duniya, daga nan kuma ya gudu da motarta samfurin Camry, talabijin, wayoyin hannu uku, Power bank da wasu kudade masu yawa.
- Yadda Tinubu Ya Yi Nasara Kan Abokan Hamayyarsa Atiku Da Obi
- Gwarzon Ɗan Ƙwallon Duniya Ta Ballon D’or: Yaushe Za A Bayar Kuma Wa Zai Lashe?
Sai dai kuma ya yi rashin nasara domin ‘yansanda sun kama shi a lokacin da yake kokarin guduwa. Ogbu ya tafka wannan aika-aika ne kwananki uku da daukarsa aiki a gidan.
Cikin watan Agusta ne ‘yansanda suka kama shi yayin da yake kokarin sayar da motar, aka kamo shi kuma ka gano cewa ashe shi wani din kasurgumin dan fashi da makami ne, domin har karamar bindiga aka samu a tare da shi.
“Saboda haka a guji yin gaggawar dauko hayar wanda zai rika yin hidima a gida har an yi kwakkwaran bincike tukunna na wanda ko wacce za a dauka aiki,”in ji Kwamishin ‘yansandan.
Ya kara da cewa a rika bincikawa shin wanda za a dauka din nagari ne shi ko kuwa?