A wajen taron manema labarai da aka yi yau Alhamis 7 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta yi karin haske kan yadda ake gudanar da shirye-shiryen babban dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na uku, wanda za’a yi a watan Oktobar bana a Beijing, inda a cewarta, kawo yanzu akwai wakilai daga kasashe fiye da 90 da suka tabbatar da cewa, za su halarci taron.
Jami’ar ta amsa tambayar da aka yi mata, inda ta ce, yau Alhamis ta cika shekaru 10 cif da shugaba Xi ya bullo da shawarar “zirin tattalin arziki dake hanyar siliki”.
Babban dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na uku, taro ne mafi kasaita da za’a yi don murnar cika shekaru 10 da bullo da shawarar “ziri daya da hanya daya” a bana, kana muhimmin dandali ne ga hadin-gwiwar bangarori daban-daban don raya shawarar tare. (Murtala Zhang)