A karshen makon jiya ne gamayyar kungiyar ‘yan kasuwa masu harkokin kasuwanci a fadin yankin nahiyarmu ta Afrika ‘Pan African Competitibeness Forum (PACF)’ ta gudanar da zaben sabbin shugabanni da za su karbi akalar shugabancin kungiyar na wasu shekaru masu zuwa inda cikin ikon Allah aka tabbatar da zabar Dakta Abubakar Tanko Bala a matsayin Babban Sakataren Kungiyar tare da wasu jami’a da za su rike mukamai daban-daban a kungiyar don samar da ci gaba mai dorewa a kungiyar.
Shi dai Dakta Abubakar Tanko Bala dan kasuwa ne kuma kararren masani mai bayar da shawarwarin yadda za a bunkasa harkokin kasuwanci, kuma a halin yanazu yana rike da mukamin ma’ajin kungiyar masu kananan masana’antu na kasa (NASSI).
- Cikar Gwamnoni Kwana 100 A Karagar Mulki: Me Aka Tabuka A Jigawa, Bauchi, Nasarawa, Gombe, Borno Da Yobe?
- A Kawo Karshen Barnata Karafunan Hanyar Jiragen Kasa A Nijeriya
Taron da aka yi inda aka zabi Dakta Abubakar Tanko Bala ya gudana ne a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jami’ar watsa labarai na kungiyar, reshen Nijeriya, Fa’iza Shehu, ta bayyana a takardar manema labarai da ta sawa hannu, ta kuma kara da cewa, babban makasudin kungiyar shi ne samar da yanayin bunkasa harkar kasuwanci da kuma ba kowa damar da yake bukata don samun nasara ba tare da takurawa ba a tsakanin ‘yan kasuwan yankin Afrika gaba daya.
A zaben da aka gudanar, Alhaji Garba Ibrahim Gusau Mni, MFR ya samu nasarar zama shugaban kungiyar ta PACF yayin da Alhaji Abdul-Fatah Shittu ya zama ma’ajin kungiyar na Afrika inda Dakta Abubakar Tanko Bala ya samu nasarar zama babban sakataren kungiyar.
Taron ya samu gaggarumin nasara, ana kuma fatan samun nasarar Dakta Abubakar a matsayin babban sakataren kungiyar zai samar da nasarar bunkasa kungiyar, saboda ganin dimbin kwarewarsa da kuma sanin makaman aikiinsa.
A tattanawarsa da manema labarai bayan an sanar da nasararsa, Dakta Abubakar Tanko ya bayyana cewa, a matsayinsa na babban sakataren kungiyar PACF zai bayar da gudummawarsa ga bunkasar kungiyar tare da tabbatar da Nijeriya ta ci gajiyar kasancewarta a cikin kungiyar ta yadda Nijeriya za ta kasance a gaba a tsakanin kasashen Afrika a fannin kasuwanci, ya kuma mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka bashi goyon bayan samun nasara, ya kuma yi alkwarin aiki tare da sauran shugabannin kungiyar don kai kungiyar ga tudun mun tsira, daga karshe ya yi alkawarin aiki da dukkan masu ruwa da tsaki wajen samar wa matasanmu aiki tare da koya musu hanyoyin dogaro da kai.