Gwamnatin Jihar Kaduna, na fuskantar barazanar tafka asarar naira biliyan 10, sakamakon bullar cutar Gansakuka da ke yi wa Citta illa, wanda hakan ya sa wasu daga cikin Manoman cittar fadin a jihar, suka bukaci a kawo musu daukin gaggawa.
Sakamakon bullar cutar a Kudancin Kaduna, Kungiyar Manoma Cittar ta Kasa (NGAN), tare da hadin guiwar wasu wadanda ba Manoma ba, sun tallafa wa Manoman Citta 18; kowannensu da naira 50,000, domin rage musu radadin annobar cutar.
- Hajjin Badi: Dalilin Kara Kudin Kujera Zuwa Naira Miliyan 4.5 – NAHCON
- Share Fagen Gasar Kofin Duniya; Messi Ya Zura Kwallo A Ragar Ecuador
Kazalika, kungiyar Manoman Cittar ta bayyana cewa, kakar noman Citta ta shekarar 2023 a Kudancin Kaduna, ta samu babbar koma baya, sakamakon bullar wannan cuta, inda ta koka kwarai da gaske a kan cewa, hakan ya yi matukar jawo asarar sama da naira biliyan 10, da ya kamata a shigar a wani fannin da ya shafi tattalin arzkin jihar.
A taron manema labarai na Karamar Hukumar Kachia da ke Jihar ta Kaduna, Shugbana Kungiyar na kasa N.B Daudu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kuma ta Jihar Kaduna, da su samar da sinadaran karya cutar ta Gansakuka.
Bugu da kari, da yake yin tsokaci a kan noman Cittar, Shugaban ya sanar da cewa, sakamakon rashin samun inda ake sarrafa Cittar, yasa ba ta iya shiga gasa a kasuwar duniya.
Daudu ya sanar da cewa, akwai bukatar a samar da inda za a rika sarrafa ta, domin kai wa wani mataki a duniya.
Ya kara da cewa, rashin sarrafa ta da kuma yadda ake hada ta, ya janyo ana barin Nijeriya a baya wajen nomanta da kuma fitar da ita zuwa kasashen ketare .
Su ma a nasu jawaban, Shugaban Karamar Hukumar Kachia Aaron Bako da kuma Daraktar Ma’aikatar aikin noma da kula da gandun daji, Kueen Saidu sun sanar da cewa, noman Citta shi ne sana’ar da al’ummar yankin suka fi mayar da hankali a kai, domin samar wa kansu da kudaden shiga.
A cewar tasu, fannin noman Citta a yankin na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara habaka tattalin arzikin wannan kasa, shi yasa muke kira ga matakan gwamantin kasar nan, da su taimaka wa Manoman Cittar a yankunan da wannan cuta ta yi wa gonakansu illa.