Sama da mambobin jam’iyyar APC dubu biyar (5,000) a kananan hukumomin Matazu da Musawa a jihar Katsina ne suka watsar da tsintsiya tare da shiga cikin jam’iyyar PDP.
Mutanen sun bi sawun jagoransu Hon. Ali Maikano don shiga cikin babbar jam’iyyar adawa a jihar biyo bayan kullin da suke da shi bayan zaben cikin gida da aka gudanar kwanakin baya.
Ali Maikano wanda ya nemi takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Matazu/Musawa a karkashin jam’iyyar APC amma ya fadi, daga bisani ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a bisa abin da ya misalta take dimokradiyya.
Da ya ke amsar masu sauya shekar a Matazu, Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, ya basu tabbacin samun adalci a jam’iyyar tare da cewa PDP a shirye take kuma tana kokarinta wajen hada kan mambobin a jihar.
Ya ce, “A yau mun amshi sama da mambobin APC 5,000 daga kananan hukumomin Matazu da Musawa karkashin jagorancin Ali Maikano da Isa Abba zuwa cikin jam’iyyarmu mai daraja ta PDP.
“A matsayinku na sabbin mambobi, ina tabbatar muku za ku samu goyon baya da adalci a wannan jam’iyyar. Za mu tabbatar kun mori kowace dama da ta samu ba tare da nuna banbanci ba”.
Da yake maida martani kan sauya shekar mambobin na APC, mataimakin shugaban APC a jihar Katsina, Bala Abu Musawa, ya kalubalanci PDP da Maikano da su bayyana sunayen mutum 5,000 da suka ce sun fice daga APC zuwa jam’iyyar adawan.
Ya misalta Maikano din a matsayin mutum Mai son kansa ba tare da duba maslahar al’umma ba, ya ce nan kusa ya san zai sake fita daga PDP din ma don kuwa a can din ma ba samun tikitin zai yi ba.