Akalla Mutum 18 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin motoci biyu kirar Mazda da kuma bas kirar Previa a kusa da gadar Isara dake kan titin Lagos zuwa Ibadan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in kula da hulda da jama’a na hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) CPEO, ACM, Bisi Kazeem, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.
Kazeem ya ce hadarin ya faru ne da misalin karfe 10:20 na dare a ranar Asabar, lamarin ya rutsa da kusan mutune 25 akan gadar Isara.
Ya yi bayanin cewa hadarin ya faru ne sakamakon keta dokar zirga-zirgar ababen hawa sannan kuma da gudu ba kakkautawa.
A cewarsa, daga cikin mutane 25 da lamarin ya rutsa da su, an iya gano maza 6, mace daya da wani karamin yaro yayin da sauran mutun 17 kuma an kasa gane su.