Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Mohamed bin Zayed Al Nahyan, a ranar Litinin a birnin Abu Dhabi, sun kammala wata yarjejeniya mai cike da tarihi, wadda ta kai ga dakatar da dokar hana ‘yan Nijeriya bizar shiga kasar Larabawan.
Bisa wannan yarjejeniya mai cike da tarihi, kamfanonin jiragen saman Etihad da na Emirates, za su dawo da zirga-zirgar tashi da saukar jiragen sama a Nijeriya nan take ba tare da wani bata lokaci ba.
Kamar yadda shugabannin kasashen biyu suka cimma matsaya da dawo da ayyukan jiragen da aka yi nan take, babu wata Yarjejeniyar biyan wani kudi ga kasar ta Larabawa nan take.
A cewar sanarwa da mai magana da yawun shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale, ya fitar a yammacin ranar Litinin, ya ce, bisa la’akari da shirye-shiryen bunkasa tattalin arzikin Nijeriya da shugaba Tinubu ke yi da kuma tsare-tsare da ya gabatar wa takwaransa na kasar Larabawan, sun cimma matsaya wacce ta kunshi zuba jari na biliyoyin dalar Amurka a cikin tattalin arzikin Nijeriya ta bangarori da dama da suka hada da tsaro, noma da sauransu.
Daga karshe, shugaba Tinubu ya yabawa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, kan kyakkyawar fahimtarsa ta hada hannu da Nijeriya don dawo da kwancen da ke tsakanin kasashen biyu.