Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da sabbin motocin bas guda 70 don jigilar jama’a da kuma saukaka zirga-zirgar ma’aikatan gwamnatin jihar zuwa wuraren ayyukansu daban-daban.
Shirin dai, an yi shine domin rage wa jama’a mawuyaciyar rayuwa da cire tallafin man fetur ya jefa su.
An gudanar da bikin ne a harabar tashar Borno Express da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Da yake jawabi, Gwamna Zulum ya bayyana cewa, wannan tallafi kashi na biyu da aka yi kan harkokin sufuri, an yi shi ne don rage radadin da ake fama da shi na cire tallafin man fetur.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, motocin bas guda 30 daga cikin 70 za a sadaukar da su ne wajen kai ma’aikatan gwamnati zuwa wuraren aikinsu daban-daban daga karfe 7:00 na safe zuwa karfe 9:00 na safe, da kuma zuwa lokacin dawowa daga karfe 3:00 na rana zuwa karfe 5:00 na yamma a ranakun Litinin zuwa Juma’a.